Wata babbar kotu a Kano ta dakatar da korar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP.
Kotun da ke karkashin Mai shari’a Usman Malam Na’abba a ranar Litinin dinnan ta yanke hukuncin kan wata takarda da ta fito daga jam’iyyar inda ta yi watsi da zargin dakatarwar da aka yi wa, Rabi’u Kwankwaso, a matsayin dan takara tare da hana hukumar zabe mai zaman kanta amincewa da dakatarwar da aka ce Jam’iyyar ta yi masa har sai an saurare shi ta bakinsa.
- Jam’iyyar NNPP Ta Dakatar Da Kwankwaso Na Wata 6 Kan Mata Zagon Kasa
- Da Ɗumi-ɗuminsa: Buba Galadima Ya Ƙaryata Batun Dakatar Da Kwankwaso A NNPP
Wandanda karar ta shafa sun hada da Jam’iyyar NNPP da kuma Cif Boniface O. Aniebonam, Gilbert Agbo Major, Barr. Tony Christopher Obioha, Comrade Ogini Olaposi, Hajia Rekia Zanlaga, Mark Usman, Umar A. Jubril da kuma Alhaji Adebanju Wasiu.
Sauran sun hada da Alhaji Tajudeen Adebayo, Alhaji Mamoh Garuba, AbdulRasaq Abdulsalam, Barr. Abiola Henry Olarotimi, Engr. Babayo Abdullahi Mohammed, Alhaji Ibrahim Yahaya, Chinonso Adiofu, Prince Sunday Chukwuemeka, Barr. Jonathan Chineme Ibeogu da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa.
Kotun bayan sauraron lauyoyin mai kara, Barr. Y.Y. Dansulaiman, Mai shari’a Na’abba ya hana wadanda ake kara ko wakilansu bayar da sanarwar manema labarai ko yin hira da su, a matsayinsu na shugabanni.