Wasu ‘yan bindiga dadi da ake zargin ‘yan garkuwa wa da mutane ne, sun yi garkuwa da Basaraken gargajiya Oloso na Oso, Oba Clement Jimoh Olukotun, a Ajowa- Akoko, da ke karamar hukumar Akoko arewa Maso Yamma a jihar Ondo.
‘Yan bindigan wadanda suka kutsa kai cikin masarautar Basaraken da karfe 10.15 na daren ranar Alhamis inda suka sace Sarkin da karfin tsiya zuwa wani wajen da ba a sani ba.
LEADERSHIP ta labarto cewa, ganau sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun Yi ta harbin iska kuma sun lalata babbar mashigar kofar gidan Sarkin kafin su samu damar shiga su sace shi.
A cewar majiyar, a lokacin da ‘yan bindigan suka isa gidan Sarkin, sun yi ta kwankwasa kofar amma aka ki nude musu Nan ne suka faffasa kofar shiga gidan Sarkin da bindiga tare da kutsawa.
Ya kara da cewa, harbe-harben da suka yi ta yi din ne suka razana jama’an yankin wanda hakan ya sa babu wani da ya isa fitowa domin kawai Sarkin dauki.
Jami’an watsa labarai na ‘yansandan jihar Ondo, (PPRO), Funmilayo Odunlami, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa tunin suka baza jami’ai domin cafko maharan da ceto Sarkin.
Odunlami ya ce, “Eh haka ne amma har yanzu cikakken bayanin ba su kammalu ba.”