• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu

by Bello Hamza
3 years ago
in Manyan Labarai, Masarautu
0
Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba 2022 ne ‘yanuwa, iyalai da abokan siyasar Marigayi Dakta Abubakar Olusola Saraki (Turakin-Ilori) wanda aka fi sani da Oloye suka taru a babban dakin taro na Chida Otel da ke Abuja don tunawa da cika shekara 10 da rasuwarsa, an gudanar da taron ne a kakashin jagorancin Sarkin Musulmi Mai Martaba Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar 111 yayin da Sarkin Ilori Mai Martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya jagoranci tawagar Sarakunan gargajiyar da suka samu halartar taron, yayin da shaharren mai jawabin nan wanda ya shahara a Afrika, Farfesa P L O Lumumba ya gabatar da jawabi inda ya gabatar da mukala mai taken ‘Muhawarar A Kan Shugabanni Da Mabiya A Afrika’.

Taron ya dauki wani sabon salo musamman ganin ana gudanar da shi ne a daidai lokacin da ake tsaka da gangamin tarukkan yakin neman zabe a sassan kasar nan na wadanda za su cike gurbin shugabanaci a shekarar 2023, amma maimakon masu shirya taron su mayar da dandalin taron ya zama tamkar wajen yakin neman zabe ko kuma wajen da za su tallata ‘yan takarar su amma sai gashi sun gaiyato kusan ‘yan siyasa daga dukkan bangarorin siyasar kasar nan, domin a hadu a kan akidar siyasar Marigayi Oloye ta kishin kasa da tabbagtar da cigaban ta.

  • 2023: Muradun CAN Da Na Dattawan Arewa A Sikeli
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Hanyar Abuja Zuwa Kogi

A jawabinsa na maraba, daya daga cikin manyan ‘yan’yan Marigayi Sola Saraki, Tsohon shugaban majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa, dalilin wannan shi ne na ganin cewa, Marigayin yana da magoya baya da wadanda ya yi tasiri a rayuwarsu a kusan dukkan siyasun kasar nan a kan haka zai zama tamkar rashin mutunci gare shi a ware wasu ‘yan siyasa a irin wannan taron. Ya ce, Mahaifinsu ya rungumi al’umma daga dukkan bangarorin kasar nan ba tare da nuna banbacin addini ko kabilanci ba, “Wannan akidar ce ta sanya a kusan dukkan inda ka ambaci sunansa sai ka samu wanda zai bayar da shaidar wani abin alhairin da ya aikata tare da kuma yi masa addu’a, mu da kanmu iyalansa har yanzu muna cigaba da amfana da ayyukan alhairin da ya gabatar a zamanin rayuwarsa, za kuma mu cigaba da amfana har zuwa ‘ya’ya da jikokinmu, saboda haka muke kira ga al’ummar Nijeriya su rungumi halayya irin ta Dakta Abubakar Olusola Saraki ta haka za a samu kasa mai cike kwanciyar hankali da son juna.’’ In ji shi.

A nasa jawabin a matsayinnsa na shugaban taron, Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad ya tuno da lokacin da ya fara saduwa da Marigayi Sola Saraki a lokacin yana aikin soja a mukamin Kaftin a barikin Soja da ke Ilori, ya ce, tun a lokacin ya fahinci mutunci da dattakunsa daga nan ne kuma suka kulla kyakyawar alaka da iyalan Marigayin har zuka wannan lokacin. Al’umma da dama na cigaba da kewar Marigayin ne saboda irin ayyyukan al’hairin da ya shuka wadanda suka hada bayar da tallafin karatu ga yaran talakawa da koya wa yaran talakawa sana’o’in dogaro da kai, wanda haka ya sa har zuwa yanzu sunansa bai bace a zukatan al’umma ba saboda yadda ya rike su a matsayin ‘ya’yansa. Daga nan ya shawarci zuriyyar da Marigayin ya bar a karkashin jagorancin Dakta Bukola Saraki, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da su tabbatar da sun rungumi akidun marigayyin, ‘Ta haka ne sunansa zai cigaba da wanzuwa” in ji shi.

A mukalar da ya gabatar, mai take “Muhawara a Kan Shugabanci da Magoya baya’ Farfesa LPO Lumumba ya yi dogon tsokaci ne a kan yadda Afrika ta fada cikin matsalar shugabanci da kuma yadda magoya baya suka kasa fahintar alhakin da ke kansu na tsayuwa tare da tsawata wa shugabanni a yayin da suka kauce hanyar da ya kamata na bunkasa rayuwar al’umma, ya ce, tun da farko Turawan Mulkin mallaka basu shirya barin tafiyar da harkokin mulkin kasashen Afrika ba, a kan haka suka dora kasashen a kan tafarkin da za su cigaba da tsoma baki a kan yadda ake tafiyar da harkokin kasa duk kuwa da sun bar mukin a hannun ‘yan kasashen Arikan ne a zahiri amma sune ke tsarawa sune kuma suke bayar da yadda za a gudanar da komai, a kan haka ne suka kafa kungiyoyi irin su na kasashe renon Birtaniya da irin na kasashe renon Faransa” in ji shi.

Labarai Masu Nasaba

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

Ya ce, dole shugabannin Afrika a wananan lokaci su farka su kuma yi koyi da halaye irin su na Marigayi Sola Saraki wadanda suka sanya cigaban al’ummar su fiye da komai, “Ta hake ne kawai al’ummar kasashen Afrika za su kubuta daga kangin Turawan Mulki Mallaka duk kwa da sun ba kasashen mu mulkin kai fiye da shekaru 60 da suka wuce’, in ji shi.

An dai haifi Dakta Abubakar Olusola Saraki ne a a ranar 17 ga wata Mayu na shekarar 1933 ya auri Misis Florence Morenike Saraki suna da ‘ya’ya hudu, sun kuma hada da Dakta Abubakar Bukola Saraki Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kwara har sau biyu da Sanata Rukayat Gbemisola Saraki wadda ta taba zama mamba a majalisar wakilai a halin yanzu kuma ita ce Ministar ma’adanai da Misis Fatimoh Temitope Edu (Nee Saraki) wadda a halin yanzu tana harkokin kasuwancinta ne a Legas sai kuma na karshe, Mista Mutairu Olaolu Saraki, wanda ya taba yi wa marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’adua mataimaki na musamman. Dakta Sola Saraki ya rasu ne a ranar 14 ga watan Nuwamba 2012 yana da shekara 79 a duniya.

Cikin abubuwan da aka shiya don tunawa da cikarsa shekasra 10 da rasuwa, akwai bayar da tallafin magani kyauta ga mabukata a garin Ilori, kaddamar da littafin tarihinsa wanda aka sama suna ‘’Sola Saraki: The Stateman’’, littafin na kunshe ne da tarihin gwagwamayar rayuwarsa na siyasa da yadda ya yi watsi da aikinsa na Likita ya rungumi siyasa da mukaman da ya rike har zuwa lokacin da ya zama Jagoran Majalisar Dattawa a jamhoriyya ta 2, lokacin Alhaji Shehu Shagari ke mulki.

Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa daga dukkan bangarorin siyasar kasar nan.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Baya Goya MarayuMarigayiSarki
ShareTweetSendShare
Previous Post

Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

Next Post

An Tsinci Gawar Wani Dan Kasuwa Mai Shekaru 37 A Otel A Jihar Bauchi

Related

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
Manyan Labarai

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

6 hours ago
Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara
Manyan Labarai

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

9 hours ago
Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina

19 hours ago
Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada

1 day ago
Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki
Manyan Labarai

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

2 days ago
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
Manyan Labarai

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

2 days ago
Next Post
An Tsinci Gawar Wani Dan Kasuwa Mai Shekaru 37 A Otel A Jihar Bauchi

An Tsinci Gawar Wani Dan Kasuwa Mai Shekaru 37 A Otel A Jihar Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

June 30, 2025
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

June 30, 2025
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

June 30, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

June 30, 2025
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

June 30, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

June 30, 2025
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

June 30, 2025
CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

June 30, 2025
Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

June 30, 2025
Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

June 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.