Sabon Jarumi me shirin zama babba anan gaba, wanda ya bayyana a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, kuma daya daga cikin Jaruman da suka taka rawa a cikin shirin Malamin Kauna.
UMAR FARUK ABUBAKAR wanda aka fi sani da UMAR FARUK NE, ya shiga masana’antar Kannywood da zafinsa, inda ya shirya wani kayataccen shiri me dogon zango wanda masu kallo ke jiran isowarsa gare su, shiri me suna AMARYAR SHEKARA.
- Yadda Ake Cin Gajiyar ‘Google Drive’ Wajen Amfani Da Kwanfuta
- An Yi Atisayen Karshe Na Dukkan Fannoni Don Share Fagen Karbar Kumbon Shenzhou-14
Jarumin ya bayyana wa masu karatu irin kalubalen daya fuskanta tun kafin shigarsa cikin masana’antar, kuma ya yi kira ga masu kallo, da masu kokarin shiga cikin masana’antar har ma da wadanda ke ciki. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka.
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi.
Sunana Umar Faruk Abubakar Sadeek wanda aka fi sani da Umar Faruk Ne.
Me ya sa ake kiranka da Umar Faruk Ne, ganin yadda aka kara Ne?
Umar Faruk Ne ya samo asali ne ta dalilin wani abokina, shi yake fada min, saboda akwai masu suna Umar Faruk da yawa kuma masana’antar mu daya.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a Jihar Yobe karamar hukumar Gulani, sunan garin mu BUMSA. Na yi karatun addini dai-dai gwargwado, sannan na yi karatun boko in da na dakata a iya Sakandare. A yanzu haka na yi aure ina tare da matata guda daya.
Ya batun ci gaba da karatu, shin za a ci gaba ko iya nan ya wadatar?
Komai nufi ne na Allah, amma dai muna sa ran ci gaba in sha Allah.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood?
Abun da ya ja hankalina yadda na ga ‘yan fim suna tura sakonninsu kuma sakonnin suna Isa kai tseye.
Wanne rawa kake takawa a cikin masana’antar?
Ina taka rawa matsayin Jarumi.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?
Eh! to ban wani dade sosai ba, ba zan fi shekara guda ba, kasancewar da waka nake lokacin ina zaune a Abuja.
Idan na fahimce ka kana so ka ce, bayan harkar fim har waka kana yi kenan?
Eh! Ina waka amma yanzu na fi bawa fim karfi.
Kafin mu je ga wakar, shin ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance, musamman yadda wasu ke kuka ga samun shigarta?
Na sha gwagwarmaya sosai kafin kasancewa ta cikin harkar, amma cikin ikon Allah mutum 2 ne silar shiga ta, wanda ba zan taba macncewa da su ba kome na zama.
Ya farkon farawar ka ya kasance, musamman yadda kake sabo a lokacin?
Na ji kamar ba zan iya ba, zuciya ta har sake-sake take min.
A wanne fim ka fara fitowa?
Na fara fitowa a fim din ‘Malamin Kauna’.
Kai ka ja fim din ko wani ne daban?
A’a! ba ni bane ina dai ciki daga wani bangaren daban.
Wanne waje ne ya fi baka wahala a cikin shirin?
Wani ‘scene’ ne muka yi da wani Jarumi har ce min yake in kwantar da hankalina, yana karamin karfin gwiwa.
Ko akwai wani kalubale daka samu daga wajen iyayenka, musamman lokacin da ka fara zuwar musu da labarin kana son shiga masana’antar?
Sosai ma dan sai da nayi kamar in hakura, amma sai na yi wa wani yayana bayani sosai ya fahimce ni, sannan shi ma sai ya yi wa mahaifiyarmu bayani ta fahimce shi, sannan aka bar ni.
Ya ka ji a lokacin da burinka ya cika?
Na ji farin ciki saboda burina ya cika na samu nasara.
A baya ka fadi cewa ka fara fitowa a cikin shirin ‘Malamin Kauna’, wanne rawa ka taka cikin shirin?
Rawar da na taka ita ce; duk wani wanda yake da matsala kowacce kala ce, idan ya same ni toh! takau matukar zai biya ni.
Daga lokacin da ka fara kawo iyanzu kayi fim sun kai kamar guda nawa?
Eh! ba su da yawa yawanci masu dogon zango ne, na yi fim za su kai kamar guda bakwai.
Ko za ka iya fadowa masu karatu sunayen wasu daga ciki?
Eh! Sosai ma, ga wasu faga ciki, akwai “Malamin Kauna, Akasi, Bawan Allah, Burin Asabe, Amaryar Shekara” da sauransu.
Duk sun fita ko kuma suna kan hanyar fita?
Eh! toh, wasu sun fita wasu kuma suna kan hanyar fita kamar dai Amaryar shekara da zai fita a ranar laraba 30/11/22, in sha Allah.
A gaba daya fina-finan da ka fito ciki,wanne fim ne ya fi kwanta maka a rai, wanda ya zama bakandamiyarka, wanda ka fi so ya fi shiga ranka, kuma me yasa?
Gaskiya a fina-finan dana fito ciki na fi son Amaryar Shekara. Ina son fim din sabida yadda labarin ya tsaru kuma shi din mallakina ne.
Kana so ka ce Amaryar Shekara kai ka shirya shi, ka dauki nauyin shirin?
Eh! kwarai kuwa gaba dayansa nawa ne, ni na dauki nauyinsa tun daga kan labarin da shiryawa da duk abin da dai ya shafi shirin ni na dau nauyi. Amma wanda ya rubuta labarin Abba Harara, wanda ya bada Umarni Ibrahim Bala.
Me fim din ke kunshe da shi, wanne sako ake son isarwa ga al’umma?
Sako ne da ake son isarwa akan masu yin auren kisan wuta,wanda suke aure akan wani wa’adi.
Shi wannan shiri na ‘Amaryar Shekara’ takaitaccen labari ne ko me dogon zango?
A’a! Me dogon zango ne, ba takaitacce bane.
Ya kake kallon yadda karbuwar fim din zai kasance ga su masu kallon, kana ganin kwalliya za ta biya kudin sabulu kuwa?
In sha Allahu, haka nake ji a raina, kwalliya za ta biya kudin sabulu, domin shiri ne daya samu ingantaccen aiki.
Kamar wadanne Jarumai ne suka fito cikin shirin?
Suna da yawa irin su; Salisu S. Fulani, Ibrahim Bala, Nasir Naba, Diamond Zahra, Momy Niger da sauransu.
Wanne iriin kalubale ka taba fuskata game da harkar fim tun daga farkon farawarka kawo iyanzu?
Gaskiya ni dai ban san ko nan gaba ba, amma a yandu ba wani kalubale.
Game da Nasarori fa wanne irin Nasarori ka samu?
Na cinma nasarori da dama.
Ya ka dauki fim a wajenka?
Na dauki fim sana’a, sannan kuma hanyar tura sako ga al’umma.
Me kake son cimma game da fim?
Suna da dama ai ina so in taimaki kaina game da ‘yan uwana da duk wani wanda muka alakantu da shi ko ta nesa ne.
Ko kana da Ubangida a cikin masana’antar?
Eh! Ina da shi, Ali Rabiu Ali Daddy
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Babban abokina shi ne; Abba Harara.
Ya alakarka take ada da kuma yanzu tsakaninka da sauran abokanka na baya?
Har yanzu babu abin da ya canza, wanda muke wasa da su har yanzu ba mu daina ba.
Bayan harkar fim kana wata sana’ar ne, idan kana yi wacce sana’a ce kuma ya kake iya hada harkar fim dinka da kuma sana’arka?
Eh! Ina wata sana’ar, ko wanne baya shafar kowanne, saboda bana sana’ar wuni guri daya ‘online business’ nake.
Da wanne Jarumi kafi son a hada ka fim da shi?
Ina so a hada ni fim da Salisu S Fulani. Abin da ya sa kuwa shi ne; Matsayina na sabon Jarumi da muka yi aiki da shi ya bani shawarwari sannan da kwarin gwiwa.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin cii ko akasin haka wanda ba za ka taba mantawa da shi a rayuwarka ba?
Eh! abun farin ciki shi ne; Ranar Aure na.
Wanne irin abinci da abin sha ka fi so?
Na fi son Shinkafa da Miya.
Wanne irin kaya ka fi son sakawa?
Na fi son Shadda.
Matsayinka na sabon Jarumi mene burinka anan gaba game da harkar fim?
Na zama babban jarumi wanda duniya take alfahari da shi.
Kafin ka fara fim ko akwai fim din daya taba burgeka, wanda har ya taba maka zuciya da har ka ji da ma a ce kai ne ciki, kuma wanne Jarumi ne gwaninka?
Abdul M Shareef shi ne Jarumi na, sannan fim dinshi ne ya fara birge ni na ji ina so in kasance ni ma daya daga cikinsu. ‘Jani Muje’ an yi abubuwa da yawa wanda suka birge ni a ciki.
Wacce shawara za ka bawa sauran abokan aikinka da suke cikin harkar har ma da wadanda suke kokarin shiga?
Mu rike amanar juna ban da yada aibun ‘yan uwanmu sannan mu daraja juna. ‘Yan baya kuma ina me kara musu kwarin guiwa.
Ko akwai wani kira da za ka yi ga gwamnati game da harkar fim?
Ya kamata gwamnati ta rinka shiga cikin lamuranmu, domin muna da mahimmin rawa da muke takawa a kasa.
Wanne kira kake da shi ga masu kallo?
Ina kira ga masu kallon fina-finan mu da su dinga yi mana adalci gurin fassara mu.
Me za ka ce da wannan shafi na Rumbun Nishadi, har ma da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina yi wa wannan shafi fatan alheri a ko da yaushe, Allah ya kara daga darajarsu sama.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina mika gaisuwa ta musamman ga masoyana na fadin duniya.
Muna godiya
Ni ma na gode.