• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Gaske Ne Annabi Muhammad (SAW) Ba Ya Kashe Wanda Ya Zage Shi?

by Sulaiman
3 years ago

LABARAI MASU NASABA

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Mutane da yawa musamman ‘yan boko akida suna ta tambaya suna cewa: “Babu wani hadisi ingantacce da Annabi (SAW) ya kashe wanda ya zage shi, hasalima akwai wadanda suka aibata Annabi a gabansa, suka zage shi amma bai kashe su, bai Kuma yi umarni da kashe su ba, don Allah malam Ya abin yake, kuma sahabbai ba su far musu ba”?
Wa alaikum assalam. Allah Yana cewa a cikin suratul Ahzaab aya ta (57): “Tabbas wadanda suke cutar da Allah da Mazonsa Allah Ya la’ance su a duniya da lahira Kuma ya tanazar musu da azaba wulakantacciya”
Ka’ab dan Al’ashraf ya kasance yana cutar da Annabi (SAW), sai Manzon tsira ya shelanta cewa wa zai isar masa game da wannan cutarwar da ake masa? Sai Muhammad dan Maslama ya ce ya Manzon Allah kana so na kashe shi? Sai ya ce na’am, sai ya tafi gidansa shi da tawagarsa, suka aika shi lahira, bayan ya yi sabuwar Amarya daga babban gida, Kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi Mai lamba ta (3811).
Annabi (SAW) ya samu labarin wani Makaho da ya kashe baiwarsa cikin dare, sai ya tambaye shi me ya sa ka yi haka? Sai ya ce ta kasance mai tausasawa gare ni, Kuma ina da kyawawan yara da ta haifa mini, amma Kuma tana aibanta ka, nakan hana ta, amma sai ta ki hanuwa, jiya da daddare na ji ta tana aibanta ka sai na samo adda sai na dankara a cikinta, na danna har ta mutu, dan da yake cikinta ya bulluko, sai Annabi (SAW) ya ce : “Ku shaida tabbas jininta ya ta fi a banza”, Abu Dawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a hadisi Mai lamba ta (4361).
Ire-iren wadannan hadisan suna da yawa, suna tabbatar da aika duk wanda ya zagi Annabi (SAW) zuwa Lahira .
Tabbas akwai munafukan da suke aibanta Annabi (SAW) a zamaninsa kamar yadda ya zo a suratu Attauba da kuma suratu Almunafikun, amma bai kashe su ba, saboda mutanen da suke gefe za su ce Muhammad yana kashe sahabbansa, saboda ba za su bambance tsakanin wanda ya shiga Musulunci da wasa ba da kuma wanda ya shiga da gaske, saboda wannan maslahar Annabi (SAW) ya kyale su, don toshe barnar da za ta iya hana wasu shiga Musulunci.
Idan mutum ya ga wanda ya zagi Annabi (SAW) bai iya jurewa ba har jami’an tsaro su karaso, ya aika shi Barzahu saboda fusata da kuma son sa ga Manzon Tsira, jinin wanda aka kashen ya tafi a banza, babu kisasi, mutukar zagin da ya yi da gangan ne, ba shi da tawili ko shubuhar da ta kasa warwaruwa, in kuma ya bayyana ba zaginsa ya yi ba, to sai ya biya rabin diyyar Musulmi, amma ba za a kashe shi ba.
Allah ne mafi sani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Next Post
Aikin Hajji Da Hukuncin Tsallake Mikati Ba Tare An Yi Harama Ba

Aikin Hajji Da Hukuncin Tsallake Mikati Ba Tare An Yi Harama Ba

LABARAI MASU NASABA

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.