Shafin da ke tattaunawa a kan batutuwa da dama na bangarori masu yawa,wanda ciki har da batun da ya shafi matasa.
Tsokacin yau zai yi magana ne akan batun da wasu masoya ke yi na Soyayya yankin azaba ce, ta yadda masoyan da suka fara soyayya ko suke cikinta ke fuskanta, musamman akan wanda suke so.
- An Yi Atisayen Karshe Na Dukkan Fannoni Don Share Fagen Karbar Kumbon Shenzhou-14
- Dalibin Da Ya Tsokani Aisha, Zai Gana Da Buhari A Villa
Wanda yake so yakan kasance kullum cikin kulawa ga abin kaunarsa ba dare ba rana, nuna damuwa da soyayya ba a cewa komai, batun sakonni a waka da kiran waya su ma ba a zancensu domin ba su da iyaka a kullum. Idan kuwa masoyin zai bayyana gidansu masoyiya ba ta da sukuni domin ganin ta faranta masa, har sauri-sauri take ya bayyana gidansu, duk wani abu da zai sa shi farin ciki ta tanada, sai dai lokaci guda wanda ake so ya kan canja akalarsa ga wani daban, wanda wani sa’in ma ta kai ga ya auri wata ko ta auri wani. Kamar dai yadda wata ta bukaci a tattauna wannan batun a shafin Taskira, wanda kuma dalilin hakan ya sa shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batun; Ko da gaske ne Soyayya yankin Azaba ce? Shin laifin waye tsakanin wanda ake so da wanda yake so din? Ko an taba cin karo da irin wannan matsalar? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sarat Alkasim daga Nijer Nagariya:
Tabbas! soyayya yankin azaba ce wata tafi ma azabar, saboda ciwon so baya musaltuwa, idan har ba ka yi dace a soyayya ba to azabar da zuciyarka za ta shiga ba ma zai yu ka misalta yadda kake ji a jiki da zuciyarka da ma duk wata kafar ruwa da jini da take gudana a jikinka. Abu ne mai matukar ciwo kaso mutum bilhakki amma daga baya ya zo ya gujeka ko kawai ya auri wata ya barka. Lefin wanda ake so ne ya ci amanar so. Hanyar da za abi dan magance hakan, yana da kyau in za ka yi soyayya kar ka zurfafa da yawa, dan gudun samun matsala. Tabbas na taba cin karo da irin wannan matsalar ta so. Shawarata ya kamata duk wasu masoya su kasance in za su yi soyayya tofa su daina nuna ta kamar za su cinye junansu, yana da kyau in za ka yi soyayya ka nemi zabin Allah kake yin addu’a a ko da yaushe, sannan ake yin soyayyar gaskiya ba ta karya ba.
Auwalu Abdullahi Umar daga Kiru:
Soyayya wata halittace da Allah (SWA) ya kagawa bayinsa da mafi akasarin al’umma ke tsintar kansu a ciki, kafin a shiga gadan-gadan za a yi ta kokarin hakan amma bayan an shiga sai ka ga halin kowa ya fito. Soyayya don Allah, jingina komai ga Allah, yin soyayya baya-baya, Tuntubar magabata da sauransu. Ni dai ban taba tsintar kaina a wannan yanayi ba sai dai makamatsnsu da ba za a rasa ba. Shawara ga matasa mu guji dogon buri,.mu nemi sana’a/aiki, mu jira lokacinmu, mu kara hakuri da rayuwa da dai sauransu.
Masa’ud Saleh Doka Dawa:
Haka ne wata soyayyar yankin azaba ce. A zahirin gaskiya babban laifin na maza ne, don sune ba sa gayawa ‘yan matan cewar ba aurarsu za su yi ba tun farkon fara soyayyar, don akwai samarin da tun farkon fara soyayyarsu da budurwa sun sawa ransu cewar ba ita suke son aura ba. Ta yi musu saboda wasu dalilai amma dai ba da aure ba, su kuma matan ba za su iya ganewa da wuri ba. Don ko sun ce saurayi ya aiko tambayar auren zai gaya mata wani dalilinsa wanda zai kare kansa da shi. Suma matan suna da ta su matsalar gagaruma don sukan raba samari gida-gida misali (my lobe, ATM, gara, dan wahala, besty, cousin, driber, bodyguard/escort dasauransu) kowanne ta san a matsayin da ta ajiye shi don in bukatarta ta taso ta wannan bangaren shi za ta nema. Guda daya kawai take so amma dukkansu za ta nuna musu sonsu take yi, sai an ce ta fidda mijin aure sannan sauran za su gane cewar ba ta sonsu. Su kuma samari wani lokacin ba laifinsu bane, ko da suna da wacce suke so a zuciyarsu da aure. Amma iyaye sukan zabar musu wata daban don wani dallina su kamar hada zumunci, aminantaka ko yabawa da tarbiyya da mutuncin yarinyar ko iyayenta. Hakika wannan yana sa samari su kasa gayawa budurwa an yi musu zabi daga gida, kuma ba za su iya bijire wa ko kin amsawa don biyayya ga iyayensu, saboda gudun kar soyayya ta yanke tsakaninsu da budurwar da suke so sai suki gaya musu cewar an zaba musu matar aure a gida. Wani lokacin kuma maza sukan canja ra’ayinsu daga baya ko da suna son budurwa da aure bayan gano wasu halaye da dabi’u wanda ba za su iya zama da su lafiya ba. Kuma ko da sun yi yunkurin nusar da su ba sa gyarawa. Hanyoyin magancewa sun hada da; binciken halayen budurwa ko saurayi tun kafin soyyaya tayi nisa. Sanar da juna abin da ke faruwa da zarar an sami matsala daga dayansu. Rage buri daga ‘yan mata don tsaida nagartaccen saurayi, ba a tara su ana tatsarsu kamar madara ba, kyautata niyya tun lokacin fara soyayyar, da tsaida gaskiya, gayawa budurwa/saurayi gaskiyar magana in ba da aure suke son juna ba. Eh! na taba samu. Shawara ba ta wuce samari su daina ko su rage kula ‘yan mata da yawa, musamman ma in sun san lokacin aurensu bai yi ba. Sannan su fara sanar da iyayensu sun sami wanda/wacce suke so kafin tafiya tayi nisa don yardar iyayen, tsayar da gaskiya da rikon amana gami da cikakkiyar kulawa, kyautatawa, mutuntawa, karrawa da nuna kishi akan wanda suke so ko ‘yan uwansu. Hakan yana matukar sa ‘yan uwa da iyaye yarda da wanda aka kawo a matsayin miji ko mata.
Abba Fagge daga Jihar Kano unguwar fagge:
Soyayya ba yankin azaba ba ce soyayya farin ciki ce, soyayya jin dadi ce tana zama azaba ne ga wadda bai yi dace ba, ko bai samu wadda yake sonshi tsakaninsa da Allah ba abin da yake sawa wani ya yaudari ko mace ko namiji sai dai idan da ma tun farko akwai dalilinsa wani daukar fansa yake akan mace wata ta taba yaudararsa sai ya rikide ya koma mayaudari akan kowace mace ita ma macen haka ne, wasu kuma sun maida yaudara ne kamar aikinsu, hakan yana sa su nishadi ko farin ciki. Hanyoyin da za a bi sune duk wadda ya zo yana sonka to ku daura soyayyar akan gaskiya tsakani da Allah sai Allah ya taimake ku. Eh! Na taba ina son wata ashe ba ta na sona ne tsakaninta da Allah ba sai dan kudi a karshe na gane hakan. Shawar kaso wadda yake dai-dai da ke wajen matsayi ko ra’ayi wadda jikinku ya zama daya shi ne.
Queen Nasmah daga Jihar Zamfara:
Soyayya ba wai yankin azaba ba ce, kawai dai shi abin da ya shafi rayuwa ko wane iri ne to tabbas akwai kalubale, ba zai yu duk a soyayya a ce ba farin ciki ba, haka zalika a ce ba bakin ciki, dole a samu biyun nan. Idan har wanda kike so ya gama cusa miki soyayyarsa a rai kika ji zai yi aure, ko wadda kake so, to a bincika dai, ko dai idan mace ce dama tana da wanda take so, ko kuma ta fahimci ba za su zauna lafiya ba ko bayan aure. Idan kuma yaudarar a fannin namiji ne, to ko dai tun dama ba sonta yake yi ba, ko kuma wani hali ya fahimta wanda hakan bai masa ba, wasu kuma suna daukar yaudarar kamar kawa ce a gare su. Hanyoyin da nake ganin za a bi a magance matsalar su ne, Na farko ki/ka san wane ne abokin tarayyarka, ka fahimce shi, ka san shin da gaske ne akwai soyayyar ko babu?, sannan a kiyaye duk wani abu da zai janyo zargi ko rashin yarda tsakaninmu. Sosai na taba tsintar kaina a cikin irin wannan yanayi. Shawarar da zan bayar shi ne ‘yar uwa ki yi kokarin ganin kin gane wanda yake sonki da gaskiya da wanda yaudara ta kawo shi.
Huzaifa Hussaini daga Zariya:
Haka yake masamman ma ace kana sonta ita kuma taki baka soyyar ta, toh! eh kin san shi lamarin aure komai na Allah saboda watakila, Allah ya rubuta hakan ita din ba matarsa ba ce ko shi din ba mijinta bane kamar yadda mutum baya auran matar wani saboda za ki ga akwai. Wanda suke soyayya kamar ba za su rabu da juna ba, amma sai ki ga iya soyayya ce kawai za su yi ba aure a ciki akwai, kuma wanda daman can shi yana sonta ne ba dan aure ba, ko dan yayi soyayya da ita ko kuma dan wata manufa nashi soyayya ai kalla-kalla ce akwai so akwai kauna toh kaunar ita ce ainihin soyayya wacce duk wanda ya rabu da daya daga cikinsu toh fa dole sai wani abu ya faru ko ta yi rashin lafiya ko yayi rashin lafiya. Shi ne kawai soyayyar gaskiya za su ci gaba da gabatar da ita domin kar su sake su juya ma kansu baya. Kuma su kara dagewa da ba soyayyar su mahimmanci, toh! ba za su samu wata tangarda ba akan tafiyarsu ba, haka ne zai kawar musu da duk wani kalubale akan soyayyar su da kuma masu zuga ta ko zuga shi kunya. Eh! toh gaskiya ni dai tawa matsalla na so wata yarinya ssi tsakanina da Allah kuma ita ma ta san na so ta tsakani da Allah, amma ita din taki ta fahimci irin son da nake mata a cikin zuciyata saboda gaskiya so da yawa Mata suna kuskure akan soyayya, kuma soyayyar Mata yana rufe masu ido akan cewa ba sa gane mai sonsu na gaskiya saboda wanda yake sonta to fa ba shi ne a cikin zuciyar ta ba ma’ana ba shi take so ba tafin wancan din wanda baya sonta na gaskiya. Toh ni dai abin da zan ce shi ne; maza karka sake ka so macce da ba ta sonka ko kuma kana sonta ba ta sonka ko ita tana sonka amma ba dan Allah ba, sai dan wani abu naka kin san Mata yanzu kafin ka samu mai sanka na gaskiya dan Allah gaskiya a yanzu dai da kamar wahala, amma dai sun ga kana da kudi ne ko kana da wani dai abu haka.
Abdullahi Muhammad Brigade Gama daga Jihar Kano:
Gaskiya soyayya yankin azaba ce domin kuwa wanda ya fada cikin soyayya ya zama kamar wani Makaho baya ji baya gani, domin ko lefin wanda yake so baya gani baya so kuma a fada. Kowanne daga cikinsu yana da laifi amma ni nafi ganin lefin saurayin domin kuwa ya san cewa har cikin zuciyar sa ba aurenta zai yi ba amma sai ya ba ta mata lokaci, kasancewar su mata kalamai suna tasiri a kansu ba lallai bane ta gane cewa saurayin nan son karya yake mata ba, domin zai nuna mata cewa duk duniya babu kamar ta, bayan kuma ba haka bane, sannan ita kuma lefin budurwar shi ne; Watakila kawaye ko ‘yan uwanta za su gaya mata gaskiya akan cewa wannan saurayin ba auren ta zai yi ba, amma kasancewa sonsa ya shiga ranta sai taki ganin gaskiyar da ake fada mata sai bayan abun ya faru kuma za ta zo tana kuka tana nadama. Hanyoyin da za a bi sune hanyoyin da addini ya tanadar, a matsayinka na uba idan wani ya zo ya ce yana son ‘yarka ka kira shi ku yi magana akan ya turo iyayensa akan a tsaida magana. sannan su kuma samari su ji tsoron Allah idan mutum ya san ba auren yarinya zai yi ba kar ya cusa mata soyayyar sa. A gaskiya ban taba cin karo da irin wannan ba, Matasa su tabbatar sun tashi aure kafin fadawa soyayya sannan su yi bincike akan wadda za su aura dan gudun gujewa yaudara.
Salis Ali daga Jihar Kano:
Gaskiya Soyayya yankin azaba ce, laifin wanda ya zo da uzurin hakurin ne, hasalima ai indai ya san haka mai zai sa ya ci gaba da soyayyar da kai, ayi Soyayya tsakani da Allah shi ne; maganin faruwar haka, sannan idan za a rabu ayi bayani. Gaskiya ni ban taba ba. Shawara shi ne; ayi Soyayya tsakani da Allah wadda za ta bayu zuwa ga Aure.
Fatima jaafar Abbas Rimin gado:
Eh! haka ne, to gaskiya kowa yanada laifi tunda akan iya samun wannan a bangaren mace ko kuma bangaren namiji, zai zama laifin mace ne a lokacin da suke tsaka da soyayya amma a cikin zuciyar ta da ma ba son gaskiya take mishi ba sai wani ya zo wanda ya fi shi sai ta ga ba za ta iya gaya masa ba don haka sai ya zama kawai sai dai ya ji labarin bikinta, haka kuma zai zama laifin namiji ne musamman idan ya je gurin mace yana sonta ne, amma ba don Allah ba wato da niyyar ( Yaudara) sai ya gudu sai dai kawai ta ji labarin aurensa. Ta hanyar yawan yin wa’azi akan hakan don da dama mutane ba su dauki hakan a matsayin wani abun laifi ba don bangaren da aka yi wa hakan yana cutuwa. Gaskiya ban taba haduwa da kalar wannan matsalar ba. Shawara ta shi ne;su ji tsoron Allah su daina son zuciya da yawan son abin duniya don ya kan janyo irin haka.