Tsohun gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya shawarci cibiyar nazarin kimiyar siyasa da ke karkashin jami’ar Bayero a Kano ta ‘Mumbayya House’ da ke gidan tunawa da Malam Aminu Kano da ta rinka gabatar da jawabi da harshen Hausa, wanda hakan zai sa jama’a su fahimci sakon da ake so a isarwa fiye da harshen Turanci.
Alhaji Sule Lamido ya bayana haka ne a wajen taron kadamar da litafun tarihin Marigayi Farfesa Haruna Wakili, tsohon shigaban gidan Mumbayya House, wanda cibiyar ta gabatar karkashin shugabancin Farfesa Habu Muhammad.
Sule Lamido ya ce ya lura da kyau ba a taba ganin taro irin wannan ba a Mumbayya wanda ya cika ya batse kuma aka dade ana taron amma jama’a ba su jagiba, kamar yadda aka saba yi a wasu tarurruka da ake yi a wannan cibiya. Ya ce amma sinrin hakan shi ne da Hausa ake yi wa jama’a jawabi, sannan taro ya shafi jama’a mafiya yawa Hausawa ne, to ya kamata a yi da Hausa in kuma na ‘yan boko ne ku yi da Turanci, amma irin wadanan tarurruka amfi cimma buri da isar da sako da harshen uwa a ko ina cikin duniya.
Taron kadamar da litafin tarihin Marigayi Farfesa Haruna Wakili, wanda ya samu halatar masana da dama da sauran masu rike da mukaman sarauta da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da sauransu.