ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Me Nijeriya Za Ta Iya Amfana A Zaben Amurka?

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
1 year ago
Amurka

Wane darasi ‘yan Nijeriya suka dauka akan kama yaran da aka yi a lokacin Zanga-zanga?

 

Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakolo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da zaben Amurka da kama yara da aka yi a lokacin zanga zanga akan tsare su.

ADVERTISEMENT

 

Fatima Abdullahi.

LABARAI MASU NASABA

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

‘yan Nijeriya za su iya amfana ta hanya dimokaradiyya da hanyar zaman lafiya da sasanci, muna sa ran wannan zaban da aka yi na Amurika ya kawo mana cigaba da zaman lafiya a kasarmu Nijeriya da sauran kasashe baki daya.

 

‘Yan Nijeriya sun dauki darasi akan yaran da aka kama lokacin zanga-zanga saboda sun sha wahala an kulle su a Abuja ba ci ba sha, daga karshe wasu daga cikinsu har faduwa suke saboda yunwa. Sai da shugaban kasa ya shiga maganar ya ce a sake su, to gaskiya wanan darasi ne babba da ya kama ta mu dauka kuma mu kiyaye gaba, zama da yunwa ba shi da dadi sannan an dauke ka cikin ‘yan uwanka kana can wani gari kana rayuwa ta kunci da azaba, iyaye sun shiga tashin hankali saboda ba su san halin da ‘ya’yansu ke ciki ba, da sun kasa bacci sun kasa ci da sha saboda fargaba ba su san halin da ‘ya’yansu suke ciki ba, suna raye ba sa raye su dai suna ta addu’a ne. Da wannan nake fadakar da iyaye da kuma ‘yan uwa da mu kiyaye gaba akan wannan lamari. Allah ya kiyaye gaba.

 

Hassan Tijjani

Wannan zabe da aka yi na Amurka muna sa ran ya kawo mana karfin Dimokaradiyya, da sanya muradin ci gaban kasa a kan kowane abu kamar yadda ‘yar takarar shugabancin kasar ta yi tawakkali da hukuncin zabe, ba tare da ta da hankali, ko kalubalantar hukunci a kotu ba.

 

Wannan kama ‘yan Nijeriya da aka yi muna sa ran ya kawo mana karfin hadin kai, tare da yin murya daya a kowane lokaci don cinma bukata.

 

Sannan kuma muma talakawa mu kiyaye duk abin da akace an sa masa doka to mu yi kokarin bin dokar shugabanni kar mu kuskura mu kusanci yin wannan abin ballantana har ya kai ga an kama mu, bin shugabanni ya zama dole ba wai su za mu duba ba, fadin Allah za mu duba bin shuwaganni shi ne bin Allah, su kuma idan sun yi adalci a kanmu sun gyautawa kansu idan ba su yi ba kansu suka yi wa, ko badade ko bajima zai dawo musu.

 

Habiba Tijjani

‘Yan Nijeriya za su iya amfana da zaben Amurka ta hanya dimokaradiyya, sannan ta hanyar shawarwari a tsakanin shuwagabannin guda biyu ta bangaren zaman lafiya da tsaro tun da shi shugaban da ya ci zaben na yanzu na Amurka ana gani shi ba me son tashin hankali bane yana son zaman lafiya, to muna sa ran samun zaman lafiya a duniya baki daya. Sannan ta hanyar cinikayya saboda shi ana ganin dan kasuwa ne to za mu iya amfana ta haka.

 

‘Yan Nijeriya ya kamata mu dauki darasi akan abin da ya faru da ‘yan uwammu na kama su da aka yi, wasu suna ganin ba su da laifi wasu kuma suna gani bai kamata a kama su ba, saboda ko suna da laifi shekarunsu ba su kai a kama su ba, to saboda haka da hukuma sun yi hakuri sun bar su tun da shekarunsu bai isa a musu hukunci ba.

 

To ya kamata ‘yan Najeriya su kiyaye su kuma guji gaba kada irin haka ta kara faruwa. Allah yasa mu dace.

 

Bilkisu Sani Amar

Assalamu alaikum. Darasin da ‘yan Nijeriya suka dauka akan kama ‘yan Nijeriya da aka yi a lokacin zanga-zanga, ya nuna hali irin na ‘yan siyasa don su nuna kyautatawa da aka yi masu don kada a zarge su ba don komai ba, kuma wannan ba zai hana a sake yin zanga-zangar ba, domin har yanzu gwamnatin Tinubu ba ta rage karin man fetur din da aka yi ba sai ma karawa da aka sake yi, saboda haka duk siyasa ce kawai dama a haka suka yi aka zabe su domin zuwa da suka yi kauyuka suka raba kayan abinci don a zabe su kamar abin arziki ashe abin tsiya ne siyasa ta zama yaudara a kasar Nijeriya domin suna yi wa kansu ne ba jama’a ba, domin da suna yi ne don kishin kasa to da ba za a samu yaudara ba, sanadiyyar karin kudin mai ya haddasa matsaloli da dama da suka hada da tsadar kayayyakin masarufi da suka hada da tsadar kayan abinci, kayan sawa wato sutura dadai sauransu. Muna fatan zabe na ga ba Allah ya zaba mana shugabanni nagari

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba
Taskira

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

November 15, 2025
Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko
Taskira

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

November 8, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu
Taskira

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Next Post
Xi Ya Halarci Kwarya-Kwaryar Taron Shugabannin APEC Karo Na 31 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Ya Halarci Kwarya-Kwaryar Taron Shugabannin APEC Karo Na 31 Tare Da Gabatar Da Jawabi

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.