Ɗan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a jam’iyyar PDP, Dakta Dauda Lawal, ya yi tir da harin da wasu ‘yan daba suka kai kan tawagarsa wanda ya yi zargin cewa gwamnatin jihar, ƙarƙashin gwamna Matawalle ce ta ɗauki hayarsu don su aiwatar da hakan.
Ya misalta harin a matsayin kololuwar karya doka da oda tare da neman haifar da hatsaniya da tashin hankali a jihar.
Lawal a wata sanarwar da cibiyar yaɗa labaransa ta fitar a ranar asabar a Gusau, ya ce, wasu ‘yan daba ɗauke da muggan makamai sun kai musu harin ne a daren ranar juma’a a lokacin da suke kan hanyar shiga Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Sanarwar ta nuna lamarin a matsayin abin kaico, takaici da damuwa, “An san PDP da mutunta doka da oda, mu jam’iyya ce da muka dukufa wurin gudanar da harkokinmu kan doka da oda. Wannan dalilin ne ma ya sanya sai da muka jira hukumar zaɓe (INEC) ta bada damar gudanar kamfen ɗin gwamna kafin mu shirya wani taron siyasa a jihar Zamfara.
“PDP ta sanya ranar 15 ga watan Oktoba domin ta amshi dubban waɗanda suka sauya sheƙa daga APC zuwa PDP, tare da ƙaddamar da kwamitin yaƙin zaɓen gwamna na 2023.
“Yan daban da Jam’iyyar APC da Gwamna Matawalle suka ɗauko hayarsu ne suka farmaki tawagarmu a kan hanyarmu ta zuwa Gusau. Motocinmu da dama an lalata, tare da kona wasu a yayin harin.
“A yau kuma ‘yan daban a ƙarƙashin wani Aliyu Alhazai Shinkafi, tsohon Shugaban kwamitin yaki da daba, kuma shugaban hukumar kula da cinkoson ababen hawa (ZAROTA) suka farmaki gidan dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP.
“Wannan sabon harin abun kaico ne inda aka kai hari kan motocin yaƙin zabenmu tare da sace duk wani abu mai muhimmanci a cikinta.
“Mun sani APC da Gwamnatin Matawalle za su iya yin komai domin kawo cikas ga harkokin siyasa da yaƙin zaɓenmu.”
Sanarwar ta bukaci Shugaban ‘yan sanda na ƙasa da sauran hukumomin tsaro da su kaddamar da bincike kan lamarin tare da shigowa cikin batun don kauce wa shigar da jama’a cikin firgici da tashin hankali.