Wani sabon rahoto daga kamfanin ‘’Ernst and Young’’ ya kiyasata cewa, bankuna 17 ne kawai daga cikin bankuna 24 da ake da su a Nijeriya za su iya tsallake sabon ka’idar da Babban Bankin Nijeriya ya kirikiro na cewa dole kowanne banki ya mallaki jarin akalla Naira biliyan 25 kafin ya ci gaba da gudanar da hakokinsa na bankin a Nijeriya. Wannan yana nuni da cewa, an yi karin ninki 15 na matakin jarin da ake da shi baya.
Rahoton ya kuma tattauna hanyoyi da mafita ga bankunan da suka kasa cika ka’idar jari da CBN ya gidaya.
- An Fara Taron Kasa Da Kasa Kan Tsarin Dimokuradiyya Karo Na Uku A Nan Birnin Beijing
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
Rahoton ya kuma tabbatar da cewa, bangaren banki na Nijeriya suna nan daram ba tare da wata barazanar da za ta iya haifar da wata fargaba ba. An fara aiwatar da irin wannan tsarin kayyade jari ne a shekarar 2023.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, wannan sabon tsarin jari da CBN ya ayyana zai kai ga hadewar wasu bankunan abin da ake kira da ‘Mergers and Ackuisitions (M&A)’, kamar yadda aka gani a lokacin da aka daga jarin bankuna a shekarar 2004 zuwa 2005. A wancan lokacin bankunan sun tashi daga 89 zuwa 25.
Rahoton ya kuma ce, “Duk da cewa, Gwamnan Babban Bankin bai yi nuni da yadda karin jarin zai shafi yadda bankuna suke gudanar da harkokinsu ba, amma an yi amfani ne da fannoni uku na tattalin arziki da kuma yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tafiya a halin yanzu. Ta haka ne muka iya gano bankunan da ba za su iya tsallake wannan siradin ba.
“A yadda abubuwa ke tafiya a halin yanzu musamman ganin an nunka jarin da ake nema daga bankuna har sau 15 to lallai bankuna 17 daga cikin bankuna 24 da muke da su ba za su iya samar da mafi karancin jari da CBN ya bullo da shi ba.”
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, shirin kara jarin bankuna ya taso ne bayan da aka karya darajar naira a wannan shekarar, ya kuma ce, a shekarar 2005 da aka yi irin wannan daga jarin bankunan, darajar naira na a matsayin N132.9 a kan Dalar Amurka 1 amma a wannan lokacin ana samu Dala 1 na Amurka ne a kan fiye da N1400.
A watan Nuwamba na shekarar 2023 ne Gwamnan Babban Bankin Nijeriya nuna sha’war kara yawan jarin da bankuna za su mallaka, ya ce, yin haka zai taimaka wajen tsaftace bangaren bankuna tare da daga darajar naira wanda hakan zai taimaka wa tattalin arzikin kasa.