ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya

by CMG Hausa
2 years ago

Shin ƙasar Sin da Turai za su iya ƙare tsarin ƙasa da ƙasa a bayyane? 

Yayin da al’ummomin kasa da kasa ke fama da ƙaruwar rashin tabbas daga rikice-rikicen siyasa, da ci gaban juna, ra’ayin da a da ake ɗaukarsa a matsayin ci gaba na ‘yantar da ƙasa da ƙasa da dunkulewar duniya, yanzu yana fuskantar babban ƙalubale. Ƙasar Amurka, a da ta kasance shugabar duniya, amma yanzu ta tsinci kanta cikin kacaniyar siyasar duniya. Kama daga tsoma baki a harkar ƙasar Sin zuwa adawa da kasar Rasha da katsalandan a Gabas ta Tsakiya, Amurka tana daɗa kunyanta kanta game da abin da take kira “kishin ƙasarta” a maimakon nazarin matsaloli ta mahangar duniya.

  • Ministan Wajen Hungary: Sin Abokiyar Hadin Kai Ce

Duk da sanin cewa rikice-rikicen da ƙasashen duniya ke ciki ya haifar da cikas ga kasuwannin duniya wanda ya haifar da koma baya a fannin tattalin arziki da yunwa, har yanzu Amurka ba ta damu da buƙatun duniya ba, musamman ƙasashe masu tasowa, ta zaɓi ta bi hanyar da ba za ta bulla ba. Lokacin da Amurka ta ga alaƙar Latin Amurka da ƙasar Sin ta bunƙasa cikin sauri, sai da ɗauki wannan alaƙar a matsayin barazana maimakon damar da za ta sanya wasu kwanciyar hankali da wadatar ƙasashen da take ɗauka a matsayin “maƙwabtarta.” A lokacin da Amurka ta ga kamfanonin Turai na ƙoƙarin tabbatar da ra’ayinsu ta hanyar zuba jari a ƙasar Sin, Amurka na kallon hakan a matsayin wata barazana da ya kamata a yi taƙa-tsantsan. Fadada tasirin ƙasar Sin zuwa ga sauran ƙasashen duniya, duk da ƙasashen duniya sun tabbatar da tasirin na taimakawa ga zaman lafiyar duniya, Amurka na kallon wannan tasiri a matsayin ƙalubale da hadari.

ADVERTISEMENT

A cikin jawaban firaministan kasar Sin yayin ziyararsa a Turai a baya-bayan nan ya ce, ƙasar Sin na ɗauke da wani ra’ayi na daban. Inda ya buƙaci hukumar ba da lamuni ta duniya IMF, da bankin duniya da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa su kammala wani sabon zagaye na yin gyare-gyare kan yawan ƙuri’u da hakkin zaɓe, da ƙara yawan muryoyin kasuwanni masu tasowa da ƙasashe masu tasowa. Ya kuma buƙaci ƙasashen da suka ci gaba da su cika alkawuran da suka ɗauka na bayar da taimako da tallafin kuɗi ga ƙasashe masu tasowa.

A yayin jawabinsa, Li ya jaddada cewa, ƙasar Sin, tare da ƙasashen duniya, sun sa ƙaimi ga samar da ‘yancin yin ciniki da zuba jari, da samar da sauki, kuma suna adawa da son kai, da wargajewa, da dakile hanyoyin samar da kayayyaki ta kowace fuska. Yayin da tsarin bai daya da son kai ke yaduwa, dole ne wani ya tsaya tsayin daka kan hadin gwiwar ƙasa da ƙasa da neman ci gaban juna.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

Ƙasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da inganta wannan tsari ga duniya. Turai a nata ɓangaren kuma, ko da yake tana fuskantar matsin lamba daga ketaren Atlantika, tana kuma neman hanyar cimma manufofin waje mai cin gashin kanta. A matsayinsu na ƙasashe biyu waɗanda tattalin arzikinsu na daga cikin manyan tattalin arziki a duniya wato ƙasar Sin da Turai, hakkin nemo hanyar ci gaban duniya ya rataya a wuyarsu.

To a daidai wannan gaɓa, sai mu ce “Dabara ta rage ga mai shiga rijiya” . (Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

November 12, 2025
Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing
Daga Birnin Sin

Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

November 12, 2025
Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
Daga Birnin Sin

Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

November 12, 2025
Next Post
Za a Fara Taron Shekara-Shekara Karo Na 14 Na Sabbin Zakaru a Tianjin a Ranar 27 Ga Watan Yuni

Za a Fara Taron Shekara-Shekara Karo Na 14 Na Sabbin Zakaru a Tianjin a Ranar 27 Ga Watan Yuni

LABARAI MASU NASABA

Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle

Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle

November 13, 2025
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su

Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su

November 13, 2025
Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule

Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule

November 13, 2025
Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna

Zaɓen 2027: Jam’iyyar ADC ta Ƙaddamar Da Kwamitin Sake Fasalinta A Kaduna

November 12, 2025
Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa

November 12, 2025
Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

Gwamnati Ta Janye Buƙatar Amfani Da Harshen Gida Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 12, 2025
Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing

November 12, 2025
Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa

November 12, 2025
'yansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi

November 12, 2025
Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci

Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci

November 12, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.