Shekarar 2024 an sha fama da sauye-sauye da rikice-rikice, kuma wasu kasashe sun rika yin barazanar katse hulda da saura, to wace hanya za a bi kuma ta yaya za a raya duniya a wannan hali? Kasar Sin na ba da amsa da mafita kan haka, wato nacewa ga manufar aiwatar da harkokin duniya tsakanin mabambantan bangarori, da gaggauta hadin gwiwar kasa da kasa da kuma goyon bayan raya kasashe masu tasowa da samun saurin bunkasa tare, matakin da zai samar da tabbaci mai dorewa ga duniya.
Shugaban kasar Najeriya Bola Mohammed Tinubu ya ce, Sin ta kasance wani babban ingantaccen karfi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. A wannan shekarar da muke ciki, shugaban Sin Xi Jinping ya yi iyakacin kokarinsa a taruka daban-daban da aka gudanar a wurare daban-daban don yin kira da kafa wata sabuwar turba ta tsaro da za ta sauke nauyin dake bisa wuyan kasashe daban daban tare cikin hadin gwiwa mai dorewa, da gaggauta tabbatar da shawarar tsaro a duniya.
Ya zuwa yanzu, wannan shawarar na samun karbuwa daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 119, ta yadda za ta zama matsaya daya dake kawo babbar ma’ana a duniya.
Bugu da kari, shugaban kasar Seychelles Wavel Ramkalawan ya ce, jerin manyan shawarwari, ciki har da shawarar tsaro a duniya da Sin ta gabatar, sun fidda wata hanya da Bil Adama za su bi wajen tabbatar da zaman lafiya da mutunta juna da cin moriya tare karkashin manufar gudanar da harkokin duniya tsakanin mabambantan bangarori. (Amina Xu)