• English
  • Business News
Thursday, May 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dabarun Samun Sauƙi Ga Magidanta

by Bilkisu Tijjani
10 months ago
in Ado Da Kwalliya, Al'adu
0
Dabarun Samun Sauƙi Ga Magidanta
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Duba da yadda abubuwa suka sake tabarbarewa, musamman idan aka yi la’akari da bangaren da ya shafi tattalin arzikin wannan, abin ba a cewa komai; domin kuwa mafi yawan magi-danta sun samu kansu a wani hali irin na ha’ula’i.

A daidai wannan lokaci, rayuwa ta zama abin da ta zama;domin kuwa komai ya yi matukar tsada, mafi yawan abubuwan da aka sani daga shekara uku zuwa yanzu; kudinsa ya ninka kusan sau uku ko hudu ko ma sau biyar, duk da cewa masu daukar albashi ba wai karuwa albashin nasu ya yi ba.

  • Babbar Sallah: Tsadar Tumatir Na Barazana Ga Armashin Bikin
  • Gwamnantin Zamfara Ta Fara Biyan Albashin Watan Yuni Domin Hidimar Sallah

Wannan yanayi da aka tsinci kai a ciki, wajibi ne ya tilasta wa maigida neman hanyar da za ta taimaka musu wajen samun sas-sauci a cikin wannan rayuwa. Don haka, ya zama lallai magid-anci ya sauya taku; ta hanyar rage wa kansa wasu hidindimu na babu gaira babu dalili. Sannan, ko da miyar da ake yi masa a gida a da sai da nama, ya kamata ya san cewa yanzu lokacin ya canza.

A bangare guda, ita ma uwargida na da tata gudunmawar da za ta bayar a rayuwrsu ta yau da kullum. Saboda haka, uwargida akwai yadda za ki hada miyarki ta yi dadi ba tare da kin sa mata nama ba, domin kuwa abin da miya ta fi bukata ita ce albasa, za ki iya yin miyarki babu nama; amma kuma ki sa mata albasa sosai, miyar taki za ta yi dadi kamar kin yi ta da nama, don ba ki sa nama a miya ba; ba shi ne zai hana miyarki yin dadi ba, rashin albasa kawai ita ce matsala.

Duk da cewa, mun shigo wani yanayi na tsadar kayan miya, musamman ma tumatur, ya yi matukar tsada ga shi kuma dole ana bukatarsa da dan yawa; wasu ma na sa shi ya fi tattasai ya-wa, saboda ya kashe zafin yaji. Don haka, a nan uwargida za ki iya sayen tattasai ya fi tumatirin yawa, idan kuma shi ma tat-tasan tsadarsa ta yi yawa; za ki iya hadawa da shambu ko kuma ma shambun zalla za kuga miyar ta yi armashi ga wadanda ba sa cin yaji. Sannan, idan kin tashi gyara shambun din ko tat-tasai; sai ki cire ‘ya’yansa da ke ciki da kuma dan jijiyar, saboda su ne suka fi yaji.

Labarai Masu Nasaba

Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?

Ciwon Mara Lokacin Al’ada

Har ila yau, akwai kuma wani salon da uwargida za ki bi wajen yin miyarki; ba tare da kin sa mata tumatur ba, za ta yi dadi kamar yadda na fada miki a baya; albasa ce dadin miyar za ku-ma ki iya amfani da tattasai ko shambun ki dan sa su da dan yawa, sai albasa ita ma ki sa ta da yawa sosai; za ki ga miyar taki ta yi kyau ta kuma yi dadi ba tare da kin sa tumatur ba.

Haka zalika, akwai kalolin abinci da dama; wadanda ba sai kin yi amfani da kayan miya ba, kamar shinkafa da wake, taliyarki idan kika samu siri-siri kika dafa ta fara, kika soya manjanki ya ji albasa; sannan sai ki kawo magi da yaji ki sa kowa da kowa a gida ya ci.

Haka nan, ita ma shinkafa ta yi matukar tsada, idan ba a samu shinkafa ba; ba dole ne sai an ci ta ba, akwai tuwon masara yana da dadi sosai; saboda haka sai ki gyara masararki a bayar a nika, domin ita amfani biyu ma ko uku za ki iya yi da ita; ko dai tuwon laushi ko burabusko ko kuma danbunta.

Kazalika, idan masarar ita ma ba ta samu ba; akwai dawa ita ma ana yin tuwo da ita, sannan kuma ga alkama ita ma amfani biyu za ki iya yi da ita; akwai tuwon laushi da kuma na buski.

Bugu da kari, sakamakon karatowar Babbar Sallah, ya kamata maigida ya sani cewa; layya ba wajibi ba ce ga wanda ba shi da hali ko iko, ballantana ya matsa wa kansa sai ya yi, illa kawai dai saboda yara za ku iya soya ‘yan kajinku; shi ma idan akwai hali, idan babu kuma sai a hakura.

Saboda haka, ya kamata uwargida ta taimaka wa maigidanta tare da kuma tausaya masa duba da wannan hali da ake ciki yanzu, har batun abincin Sallah, idan babu hali ba dole ne sai kin kashe kudi mai yawa ba, duk abin day a samu sai a yi hakuri a karba a haka; wata rana sai labari.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: FoodFoodsRagoRamsSallah
ShareTweetSendShare
Previous Post

Arsenal Ta Kammala Ɗaukar Riccardo Calafiori Daga Bologna

Next Post

Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar

Related

Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?
Ado Da Kwalliya

Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?

4 days ago
Ciwon Mara Lokacin Al’ada
Ado Da Kwalliya

Ciwon Mara Lokacin Al’ada

4 days ago
GORON JUMA’A 16/05/2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 16/05/2025

6 days ago
Maganin Kurajen Fuska
Ado Da Kwalliya

Maganin Kurajen Fuska

3 weeks ago
Me Ke Sa Amare Yin Watsi Da Kwalliya Idan Sun Kwana Biyu A Gidan Miji?
Ado Da Kwalliya

Me Ke Sa Amare Yin Watsi Da Kwalliya Idan Sun Kwana Biyu A Gidan Miji?

4 weeks ago
Maganin Karin Kiba
Ado Da Kwalliya

Maganin Karin Kiba

1 month ago
Next Post
Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar

Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar

LABARAI MASU NASABA

Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 

Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 

May 22, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa

May 22, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

INEC Ta Samar Da Sashen Ƙirƙirarriyar Basira Domin Inganta Harkokin Zaɓe 

May 22, 2025
Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya

Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya

May 22, 2025
Sanata Adamu Aliero Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Ga Ƙananan Hukumomi Takwas A Kebbi

Sanata Adamu Aliero Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Ga Ƙananan Hukumomi Takwas A Kebbi

May 22, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Tiriliyan 1.5 Don Magance Matsalar Abinci — Minista

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Tiriliyan 1.5 Don Magance Matsalar Abinci — Minista

May 22, 2025
Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur

Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur

May 22, 2025
Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan Crypto 

Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan Crypto 

May 22, 2025
Tsaro Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Bunƙasa Tattalin Arziƙi – Atiku

Tsaro Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Bunƙasa Tattalin Arziƙi – Atiku

May 22, 2025
Ma’aikatan Wutar Lantarki A Katsina Sun Tsunduma Yajin Aiki

Ma’aikatan Wutar Lantarki A Katsina Sun Tsunduma Yajin Aiki

May 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.