Shafin da ke tattaunawa akan batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; Zamantakewa na rayuwar yau da kullum, Zaman Aure, Rayuwar Matasa, Soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu mazan ke saba alkawarin da suka daukar wa kansu, musamman a kan matan da za su aura.
Akwai maza da dama wadanda suke yunkurin auran matan da suke da yara, tare da yi musu alkawarin za su rike ‘ya’yan da suke tare da su, bayan aure ya tabbata zama ya yi nesa sai zance ya sha bamban. Sabani da tashin hankali ya yawaita, har ya kai da mijin ya nemi ta zabi guda cikin biyu, ko shi ko ‘ya’yan da ta je da su cikin gidan, wanda kuma hakan ke sawa matan su zabi zama da yaransu madadin mijin, karshe dai aure ya mutu.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me ya sa mazan su ke yin hakan?, ta wacce hanya ya kamata mata su bi wajen zabin mijin aure, musamman masu irin wannan matsalar?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Princess Fatima Zahra Mazadu Jihar Gombe:
Ga dan tsokaci kadan kafin na shigo babin amsa; Wannan dai da farko rashin sanin ya kamata ne, dan ba mai kin dan wani sai jahili mara tunani dan da na kowa ne, baka san mai amfanarka ba, naka ko na wani, maza sun maida abun ado wai a zabe su ko a zabi ‘ya’ya? Allah shi kyauta, wannan abu da sun san girman zunubinsa da za su kiyaye ko an ce su furta ba za su furta ba bare su aikata.
Toh game da wannan maidu’in wallahi abun takaici ne, dan a wannan yanayin mata suna samun rayuwa mai kuncin gaske har su sanya a zuciyar su mazan duk duniya haka suke ne ko sune ba su da sa’a da rashin dacewa da mazan da suka san girman alkawari?. Gare ku mata, Furta kalmar zaban yara akan miji babban laifi ne ko da alkawarin ko babu, gwara gyara ta wani fanni da gaskiyarsa in ya ce ba zai rike ba, amma anan shi randa ya bar nashi wa zai rike masa? Ga girman alkawari, chaf di jam, Rike dan wani riba biyu ne, ya amfane ka sannan ya amfani zuriyarka da yayanka, amma wasu mazan sun kasa fahimta sam!.
Eh toh wasu maza na cewa wai in ka rike dan wani shi zai zo ya kashe ka daga karshe, in ji hausawa, amma wannan duk shiririta ne, ba mai kashe bawa sai Allah da ya halicce shi, shi dai zama da Agola sai hakuri, saboda komai za ka yi hankalin mamansu na kai, in ka tsawata ta ce ka tsane su, in kayi sanyi ka zuba musu ido ta ce baka son su, sannan an dinga na-na-ta maka alkawari ka dauka, dole hakan yana damunka, to zama da abun da baka haifa ba sai addu’a da kulawa, ya zama ba bambanci da abun da ka haifa. Babu hanya sai guda daya tak! addu’a shi ne jigo, sannan kuma sanannu a zamantakewa, hakuri da juriya, gidan in ba na maihaifinka bane dole sai kayi hakuri, dan koda maihaifinka ne kai ma ba zai so bari ya bar ka ba.
Shawara daya ce ka daina alkawarin da kai ka san ba za ka cika ba, dan Adam ne kai ajizi, Allah kadai ke iyarwa bawa, duk son da ka ke wa mace kar ka sake kai mata alkawari dan wallahi duk wuya sai ka cika mata maganin bari kar a fara, ake gina gaskiya cikin duk al’amura dan Allah.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Wannan abin yana faruwa a rayuwarmu ta yau da kullum, amma gaskiya abu ne wanda bai dace ba, sannan kuma ba hali ne mai kyau ba, don babu tausayawa a cikin. Ba komai bane illa yaudara, don biyan bukatarsu kawai suke aurar matan daga baya su ce ta zaba miji ko ‘Ya’ya, don ba yadda za ta yi. Hanyoyin da za a bi sune; Tabbatar wa da manemin cewa tana da ‘ya’ya da kuma adadinsu, sannan bin hanyar da za ta rage wa mijin dawainiyya da yaran. Shawara ita ce; su ji tsoron Allah su daina, sannan kuma su gaya wa matan gaskiya kafin auren, cewa; ba za su iya daukar nauyin ‘ya’yan ba tun kafin ma a fara, sannan su sani cewa za su iya mutuwa su ma su bar nasu, matan da ‘ya’yan, in ka ji kan na wani, kai ma Allah zai kawo wanda zai ji kan naka.
Sunana Fauziya Usman (filsakcollection) daga Jihar Adamawa (Jimeta/Yola):
Abin da zan ce a game da wannan maudu’in shi ne; Gaskiya mazan yanzu majoriti ba sa son ‘ya’yan wani, za su ce suna son mace amma fa ba sa son ‘ya’yanta na gidan wani mijin, kuma ni abin da na fi la’akari a kanshi shi ne, su mazan suna ganin in har ya auri mace da ‘ya’yanta yana ganin za a bar mishi dawainiyan yaran ne shi ya sa suke nuna ba sa ma son yaran kwata-kwata. Mace indai har za ta zabi mijin aure kuma tana da ‘ya’ya bai ma kamata ta auri mutumin da zai nuna ba ya son ‘ya’yanta ba, ai in shi ne yake da ‘ya’ya yana so ita macen ta rike mishi nashi, amma shi ba zai iya rike mata nata ba, kwana biyu sai ace an yi saki, kuma duk akan ‘ya’yan ne, don mace ba za ta zabi zama da mijin akan ‘ya’yanta ba. Shawaran da zan ba wa Maza masu irin wannan hali don Allah su daina, watakila su ma ‘ya’yan ba wai son ransu bane suka tare a gidanka, watakila marayu ne ba su da uba, kai ma kuma hakan na iya faruwa da kai kuma ba za ka so a yi wa ‘ya’yanka haka ba, Allah ya sa mu dace duniya da lahira.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano, Rano:
Na farko soyayya ce ke saka namiji ke gayawa macen hakan kamar yadda karin maganar malam bahaushe da yake cewa; “DADIN ZAMA – KEbSA A CEWA MIJI BABA”, to idan kuma an zo zaman yau da kullum sai abubuwa su canja. Na 2 kuma wani koda ana zaune lafiya to ita matar ita ce take kokarin dorawa mijin nauyin wasu abubuwan da shi kansa mijin ba lallai ace zai iya yin su ba duba da ba shi ne asalin uban yaran ba, to daga nan ita kuma hajiya madam sai ta yi fushi. Wasu mazan suna canja alkawar ine duba da sun ga sun sami abin da suke nema wato ita uwar yaran, sannan wani lokacin kuma kamar yadda na gaya a sama ne ko zaman ya canja ko kuma dorawa mai gidan nauyin yaran da uwarsu take yi eanda wani magidancin ma sai ka ga koda yaransa na cikinsa ba sa samun waccan kulawar da ita uwar yaran take so ya yi wa nata yaran. Hanya daya ce addu’a da neman zabin Allah, domin maganar gaskiya daga mu mazan har matan ba a gane halinmu na gaskiya a zaman aure har sai an yi, musamman a wannan zamanin duba da mafiya yawanmu muna saka karya da son kanmu wajen fahimtar da halayenmu kafin daura aure. Shawarata anan ita ce su ji tsoron Allah kuma su tuna cewa su ma za su iya haifar nasu yaran, kuma su je su yi tasu rayuwar a gidan wani babu wanda zai so ya haifi yaro ya ga ya wulakanta, sabida ko babu rabuwar aure to akwai mutuwa. Don haka mu ji tsoron Allah mu rike amanar duk wani yaro ba ma iya na gidanku ba koda na gari ne da ma unguwa, sabida shi yaro ba a san iya mai morarsa ba. Allah ya sa mu dace.
Sunana Bilkisu Yakubu (Bestie) Jihar Bauchi:
Ni dai abun da zan ce anan macen da take da yara kar ta dogara da mijin da za ta aura, ta zamto me neman na kanta shi kansa mijin in ya ga tana kokarin neman na kanta to zai ji kwarin gwiwar yin Auren, mata mu nemi sana’a don kare mutuncinmu. Su kuma maza masu wannan halin da ma tun farko ba auren tsakani da Allah suke yi ba, kawai don cimma wata burinsu ne daga zarar sun cika sai su gudu. Maza a ji tsoron Allah, wallahi baka san waye zai taimake ka ba, ko ba yaron matarka ba wani ne daban tabbas! ka taimake shi to ba zai taba faduwa kasa banza ba, domin alheri ba ya tafiya a banza komai dadewa sai ka ga sakayyarsa, domin ka kan haifi da ba za ka more shi ba wani dabanne zai mora shi, kai kuma dan wani ya more ka, ubangiji yabsa masu yin hakan su gane.
Sunana Mzee Kano:
Soyayya ce take rufewa maza ido suke ganin duk wuyar abu me sauki ne a gare su, indai za su mallaki yarinya sai daga baya su ke gane babban aiki ne suka dakko , wanda hakan zai zama takura a cikin rayuwarsu, shi ya sa mazan suke ba su zabi shi kuma yaro da uwa sai Allah, shi ya sa matan suke hakura su zabi ‘ya’yansu dan in suka bar su ba su san wanne hali za su fada ba. Shawara ga mazan da suke haka ya kamata kafin su dau alkawarin hakan su duba gaba su duba baya in mutun ya san ba zai iya ba kar ya dau alkawari, in ko ya dauka to ya daure ya kau da kai ya rike. Saboda yaro na kowa ne, kuma shi ma bai san ya rayuwar yaronsa za ta kasance a gaba ba, Allah ya sa mu dace.
Sunana Bilkisu Muhammad:
Mazan soyayya ce take rufe musu ido sai suna gani ko idan ba su ce za su rike mata yaran ba kamar ba ta aure su ba, ke kuma kina gani ga wanda ya ce zai rike miki yara to bari na aure shi, dan Allah maza kuna yin abin da za ku iya, mata kuma suna nutsuwa wajan zabar mijin aure, tunda ke ba yarinya bace.
Sunana Misbahu Muhammad Gorondutse Kano:
Hakan ba daidai ne ba, domin shi Alkawari kaya ne. Tsabar yaudara da son mallakar wacce suke son su Aura ne. Idan namiji ya zo neman Aure kuma ya yi alkawarin zai rike miki ‘ya’ya to ya kamata a sanar da wakilansa tun kafin a daura Auren. Ya kamata maza su sani cewa zalunci ne kayi alkawarin da ka san ba za ka iya cikawa ba.
Sunana Zara Muhammad Sunusi (Ummu Heebbat), Gaidam Jihar Yobe:
Ni a nawa tsarin gaskiya matukar zan auri mutumin da ya ce zai rike min yara, to sai na yi bincike kamar haka a kansa; Shin yana da dukiya daidai misali?, ma’ana ya fi karfin gidansa ko kuma ace ba shi da wasu yaran daman shi mutum ne mai son yara. Sannan ace yana da halin kirki 99% an san haka, to zan yi garajen gwadawa hadi da addu’a. Abin da ya ke sanyawa maza su yi haka shi ne; wasu daga cikinsu daman ba su da halin rike yaransu ma bare kuma agola. Kawai sun fadi haka ne saboda su samu su auri macen idan ya so daga baya komai ta fanjama-fanjam. Wani kuma shi daman can ya ganki yana so ne kuma ga yara ba zai iya rabuwa da ke ba, amma kuma da man shi ba mai son yara bane shi ne zai yi amfani da damar shi wajen dadin bakin zai rike miki su ya yaudare ki har a yi auren daga baya ya nuna miki asalinsa. Shawarata a gurin macen da ta ke da yara za ta yi aure shi ne; Ta zama tana da abin yi, ma’ana ta zama tana da sana’ar da za ta rike kanta da yaranta wanda ko da miji ya far miki wulakanci kina da ma da fa. Saboda shi kanshi mijin da za ki aura matukar kina da wani abu ya aure ki wallahi ba lalle ya yi miki haka ba, musamman idan yana samun abincin da ya fi karfin cefanensa, saboda yanzu rayuwar ta canja. Mazajen da suke haka su ji tsoran Allah, su sani za su mutu su ma, kuma haka za a yi wa yaransu idan a ka je da su gidan wani, dan haka ko dan wannan ma ya sa maza su yi hakuri indai har sun ambaci za su rike to kawai su rike din, maganin kar a yi – to kar ma a fa ra. Idan har sun san ba yi za su yi ba, to su hakura da auren matar ko su fada mata asalin gaskiya.