Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta yi nasarar cafke wani mutum mai suna Linus Dimas, dan shekara 43, bisa zargin yi wa magatakardar Kotun Yanki kisan gilla a garin Kugama Wuro-Jibir, cikin Karamar Kukumar Mayo-Belwa a Jihar Adamawa.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Suleiman Yahya Nguroji, ya aika wa manema labarai ta ce “Ranar Litinin, Linus Dimas, ya ki amsa gayyatar da kotu ta aiki magatakardar tata Ya’uba Usman ya kai masa.
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas: Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
- Kamfanin Man Nijeriya Ya Sa Hannu Kan Fasahar Gano Sinadarin Methane
“Ya’uba Usman, ma’aikacin kotun yanki da ke Nasarawo Jereng, wanda ake zagin ya yayyanke shi da wuka a wurare da dama a jiki, da ya samu raunuka masu tsanani.
“An yi gaggawar kai Sakatare Ya’uba asibiti, amma aka tabbatar ya mutu” in ji sanarwar SP Suleiman Ngruroje.
Yahaya Nguroji, ya ce tuni kwamishinan’yansandan jihar CP Afolabi Babatola, ya yi umurnin gudanar da cikakken bincike kuma a tsanake kan lamarin.