“Duniya na sauya salonta. Me ya kamata mu yi don fuskantar duniyar da kasashe daban daban ke tabbatar da ci gabansu na bai daya?” An gudanar da taron shekara shekara kan harkokin tsaro a birnin Munich na kasar Jamus a kwanan baya, kuma faifan bidiyo na tallata taron ya mika wannan tambaya ga mahalarta taron. Kafin budewar taron kuma, masu shirya taron sun gabatar da rahoton tsaro na Munich na shekarar 2025 wanda ke da taken “bunkasar kasashe daban daban na bai daya”, wanda yake ganin cewa, “bunkasar kasashe daban daban na bai daya ya zama tabbas.”
Kusan a lokaci guda ne, aka gudanar da taron kolin kungiyar tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa, taron da aka sanya wa taken “tabbatar da adalci ga ‘yan Afirka da zuriyoyinsu ta hanyar biyan diyya”. Kasancewarta nahiyar da aka fi samun kasashe masu tasowa a duniya, yadda kasashen nahiyar suka fito da muryarsu ta tsayawa kan kafafuwansu da ma gyara kura-kurai na rashin adalci a gare su, shi ma ya shaida mana karatowar zamanin da kasashe daban daban ke tabbatar da bunkasarsu ta bai daya.
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 2 Da Ake Zargi Da Yi Wa Yarinya ‘Yar Shekara 12 Fyade A Yobe
- Ƴan Ta’adda Sun Sako Manoma 11, Sun Rike 3 A Borno
A cikin shekaru daruruwa da suka gabata, kasashen yammacin duniya sun bunkasa bisa ga tarin dukuyoyin da suka kwace daga kasashen Afirka, lamarin da ya sa har yanzu al’ummar kasashen Afirka ke fuskantar talauci. Sai dai ba a kai ga gyara wannan yanayi na rashin adalci da ake ciki a karkashin tsarin duniya da kasashen yamma ke jagoranta ba. A wannan karon, kungiyar tarayyar Afirka ta gabatar da bukatar gyara kura-kuran, kuma hakan ya faru ne daidai saboda yanayin da suka samu kansu a ciki na bunkasar kasashe daban daban, musamman ma yadda kasashe masu tasowa suka kara karfinsu har suka fara taka muhimmiyar rawa a duniya.
A hakika, ba kudade kawai kasashen Afirka suke bukatar a biya su ba, suna kuma neman wargaza irin tsarin tattalin arzikin da suke dogara ga kasashen da a baya suka yi musu mulkin mallaka, wato irin tsarin wawushe albarkatunsu da aka kafa a lokacin mulkin mallaka har yanzu suna aiki. Alkaluman da MDD ta samar sun shaida cewa, nahiyar Afirka na da kaso 30% na ma’adinan duniya, sai dai yawan cinikin da kasashen Afirka suke yi bai kai kaso 3% na duniya ba, kuma kayayyakin da suke samarwa ya kai kaso 1.9% na duniya ne kawai. Daidai kamar yadda Mr. Claver Gatete, sakataren zartaswa na kwamitin kula da tattalin arzikin Afirka na MDD ya fada, abin da ake nufi da biyan diyya shi ne, ya zama dole albarkatun Afirka su amfana wa Afirka, kuma a kafa masana’antu a kasashen Afirka, a fadada tsarin masana’antu a kasashen.
A yayin da yake halartar taron tsaro na Munich na wannan shekara, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi nuni da cewa, ya kamata a wanzar da adalci da oda a yanayin da duniya ke ciki na samun bunkasar kasashe daban daban. Ya jaddada cewa, kiyaye adalci ta fannonin ikon kasa da kasa da damammakinsu da ma ka’idojin da suke bi, ya kamata ya zama tushen gina duniya da kasashe daban daban ke tabbatar da bunkasarsu ta bai daya. A hakika, kasancewarta babbar kasa mai tasowa wanda ke goyon bayan bunkasar kasashen duniya na bai daya, har kullum kasar Sin na neman kyautata wakilcin kasashe masu tasowa, musamman na kasashe Afirka, a tsarin duniya, tana kuma kokarin more damammakinta ga kasa da kasa, don tallafawa bunkasuwar kasashen duniya na bai daya. A game da hakan, tsohon ministan harkokin wajen tarayyar Nijeriya, Ibrahim Gambari ya ce, kasar Sin ita ce ta farko a duniya da ta bayyana a fili goyon bayanta ga shigar kungiyar tarayyar Afirka G20, matakin da ya shaida yadda kasar Sin ke goyon bayan kasashen Afirka wajen kara fitowa da muryarsu a duniya.
Bunkasar kasashen duniya na bai daya ya zama tabbas, wanda kuma yake tabbata. Kamar yadda shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bayyana a wajen taron tsaro na Munich, “Kasashe daban daban na tabbatar da bunkasarsu yanzu a maimakon yadda muke a baya. A lokacin da aka kone tsoffin gadoji, ana gina sabbi…kuma ya kamata mu sake hada kasashen duniya bisa wadannan sabbin gadoji.” (Lubabatu)