Hukumar Kula Da Jin Dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta ce, hukumomi a kasar Saudi Arabiyya za su amshi ragamar kula da ciyar da maniyyata da samar musu da masauki a Makka da Madina, lamarin da zai fara kasancewa daga aikin hajjin 2025.
A wata sanarwar da kakakin NAHCON, Fatima Usara, ta fitar a makon jiya, ta ce, an cimma wannan fahimtar juna ne a wani tattaunawa ta yanar gizo da aka gudanar a tsakanin hukumar da ma’aikatar kula da aikin hajji da Umrah (MoHU) ta kasar Saudiyya.
- Kaso 40 Na ‘Yan Nijeriya Na Samun Wutar Lantarki Fiye Da Awa 20 A Kowace Rana — Minista
- APC Ta Lalata Nijeriya, PDP Kuma Matacciyar Jam’iyya Ce — Kwankwaso
Fatima ta kuma kara da cewa hukumar ta gudanar da ganawar fara shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin da ke tafe da manyan sakatarorin kula da jin dadin alhazai na jihohi, wanda kwamishina a NAHCON, Anofi Elegushi ya jagoranta a ranar 23 ga watan Satumba.
A cewarta, Elegushi ya ce kamfanonin da hukumar alhazan Saudiyya ta assasa da aka fi sani da ‘mu’assasa’, su ne za su kula da ciyar da alhazai da samar musu da masauki a Makkah da Madina da zai fara daga 2025 bisa kulawar ma’aikatar MoHU.
“Wannan tsarin zai shafi dukkanin kasashen da za su halarci aikin hajji, kuma zai fara ne daga aikin hajjin 2025,” ya shaida.
Elegushi ya jaddada aniyar NAHCON na fara gudanar da shirye-shiryen aikin hajji bisa lokacin da Saudiyya ta bayar, kuma ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki kan aikin hajji da su bayar da hadin kai.
Shugaban kungiyar jagororin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, Idris Almakura ya yaba wa NAHCON kan kokarinta da take kan yi, ya roki hukumar da ta ci gaba da daukan kyawawan tsare-tsaren da take bi.
Almakura ya nuna damuwarsa kan tsarin ajiyan kudin kujera, tsarin tawagar jami’an kiwon lafiya da kuma tsarin jinkirin maida wa maniyyata kudadensu.
Da yake maida jawabi, Elegushi ya yaba wa jagororin kula da aikin hajji na jihohi kan yunkurinsu na sanar da tsarin ajiyar kudin aikin hajji da wuri, ya shawarcesu da su amshi wasiko kan yawan kujeru da kuma lasisi na aikin hajjin 2025.