Bisa sanarwar da kwamitin kula da harkokin harajin kwastam na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda, game da karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga kasar Amurka, da matakan karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga kasar Amurka, tun daga karfe 12 da minti 1 na yau Alhamis 10 ga watan nan na Afrilun shekarar 2025, an fara karbar karin harajin kwastam na kaso 84 bisa dari kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga kasar Amurka. (Mai Fassara: Maryam Yang)














