Mutuwar wani matashi mai shekara 24 mai suna Hamza Adamu a kauyen Tungan Tsauni da ke karamar hukumar Tafa ta Jihar Neja a ranar 13 ga watan Afrilu 2022 ta bar baya da kura, domin kuwa duk da cewa, rundunar ‘yansandan Jihar Neja sun kama mutum biyu da ake zargi da aikata wannna mummuna aiki (Abba Yakubu da Umar Abdullahi da aka fi sani da Dady) amma har zuwa yanzu an kasa sanin halin da Kes din ke ciki, kuma ‘yansandan sun mayar da mahaifin mamacin mai suna Adamu Shu’aibu tamkar saniyar tasta, duk wani motsi da za a yi a kan lamarin sai sun nemi kudi daga gare shi.
A halin yanzu yana fuskantar tashin hankali kala-kala, gashi ya rasa dansa, kuma gashi yana ta asarar kudade ba tare da ya san yaushe za a fitar wa da dan nasa hakkinsa ba. Mataimakin Edutanmu Bello Hamza ya tattauna da Adamu Shu’aibu inda ya yi cikakken bayani na yadda lamarin ya faru, haka kuma mun ji ta bakin jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansandan Jihar Neja DSP Wasiu A. Abiodun inda ya yi tsokaci a kan lamarin.
Yadda Lamarin Ya Faru
“Wato abun da ya faru, da na ne ke neman aure a nan kusa da kauyenmu, ni ina Tungan Tsauni su kuma suna Sanali, kuma yarinyan da yake neman aure din duk garin babu mai neman ta, ‘yar mai unguwan kauyen ne. Sai da na yaje ya nema suka amince mashi suka karbi kudin gaisuwa suka karbi dukkan abin da ake karba na aure har da sadaki, suka amince da bashi auren yarinyar, kawai ana jiran lokacin da za a yi biki ne.
A Musulunce idan aka ce an baka yarinya to bai kamata ta saurari wani kuma, bai kamata iyayen ta su bari ba. Ni kuma a nawa tsarin ban yarda yarinyar zo gida wurin ba ko kuma shi ya je tadi da daddare.
Na hana wannan, saboda za a ga kaman suna wani fitsaranci ne a waje. Kaga bai dace ba. Yarinyar ta ce za ta zo nace, sai nace a’a. Sai dai shi ya je duk abin da take so ya yi mata a can ya rabu da ita a gidan iyayenta.
A ranar da abin ya faru, ana cikin azumin Ramadan da kwana 12, ya tafi don ya gana da yarinyar, sai ya samu wani tsaye tare da yarinyar, sai ya ce waye wannan? Da ya tambayi waye wannan sai ta ce ba abin da ya hada su.
Ya gama abin da ya kaishi ya bata abin da kai mata, yana kan hanyar dawowa gida sai wannan yaron ya tare shi a hanya yana tuhumarsa a kan wai mai yasa zai tambayi yarinyar abin da ya kawo shi wajenta, sai ya mayar masa da amsar cewa, menene laifi a nan, na ganka tare da wanda zan aura ne shi yasa na tambaya waye, tan kuma ta yi mani bayani ai kaga na yi shiru na kyale ka.
Duk da an shiga tsakaninsu an raba su amma sai da ya daga hannu ya mari yaron nawa, da zai rama sai mutane suka bashi hakuri, ya tafi. Sai ya bi maganan mutane ya biyo hanya ya koma gida. Sai wancan yaron ya kira abokansa suka bishi har kusa da gida suka kama shi da duka suka caccaka masa wuka a nan suka kashe shi”.
Magana Ta Koma Hannun ‘Yansanda
“Nan take aka kira ‘yansanda suka nemi a kai gawar yaron asibiti suka ce, tun daga nan kuma suka fara karbar Naira dubi 5 a hannun na.
Da safe suka zo, sai suka ce a kawo mai daukar hoto shima said a bayar da dubu 4, sai kuma wata dubu 4 da sunan rubuta ‘Statement’, suka kuma sake neman wata dubu 4 da cewar za a sake daukar wani hoton kuma, wanda kaga ai duk hakkin ‘yansandan ne, daga nan kuma suka bukaci in kawo dubu 4 da sukan wai za a je inda suka fara fadar a sake daukar hoto kuma ni zan biya, haka kuma sun karbi Naira dubu 4 a hannu na na kudin karbar takardar shaidar mutuwar yaron (Death certificate) daga asibiti.
Ana cikin haka suka sake karban Naira dubu 8 a matsayin kudin mota zuwa ofishin sun a Sabon Wuse, da aka nemi in rubuta ‘Statement” na rubuta musu cewa, ina gida zaune bayan na idar da salla sai wani yaro ya shigo gidanmu a guje yana ihu cewa, an kashe Hamza da fito kuma naga lallai gasiya ne an kashe shi, abin dana rubuta musu kenan”.
An Farauto Makasan Yarona
Daga na aka fara farautar Abba Yakubu da Umar Abudllahi Barau (Dady), yaran su biyu da ake zargin kashe mini yaro, inda ba tare da bata lokaci ba aka kama daya bayan kwana biyu kuma aka samu nasarar kama daya yaron shi ma, an dan sha wahalar kama yaron domin iyayensa sun boye shi a wani kauye har sai da aka kama su kafin aka fito da shi. Bayan ‘yansanda sun dauki ‘Statement dinsu tare da na yarinyar sai aka wuce dasu ‘State CID’ da ke Minna ranar wata Litinin, da za mu tafi sai suka ce ni zan biya kudin mota zuwa Minna, daga baya kuma suka ce suna da mota in kawo kudin mai Naira dubu goma daga nan ne na fara tunani, na rasa yaro kuma ina ta biyan kudi, ai su iyayen yaran da suka yi kisan yakamata su dinga daukar nauyin dawainiyar da ake yi, amma dai na cigaba da zura ido.
Da muka je Minna din aka sake daukan bayanan mu. Da muka gama a wajen, yan sandan da muka je dasu suka nemi kudin abinci, sai da na basu Naira 500 kowannensu.
Da aka gama sai suka ce za su rike yarinyar, muka nemi a bamu ita, a kan haka said a suka karbi Naira 10.
Har Yanzu Babu Wani Labari
Wallahi tun da muka dawo yau wata biyu kenan sai ranar suka kira ni wai in same su a ofishin ‘yansanda na Suleja daga zuwa kawai suka ce in kawo kudi, nace kudin me zan kawo muku? Suka ce za su yi shattar mota su zo su ga wurin da aka yi kisan.
Na ce wani irin wurin da aka yi kisan, duk da hotuna da kuka dauka na wurin da aka yi kisan? Daga nan ne na ce ba zan bayar da ko-kwabo ba. tun daga ranar kuma ban sake ji daga gare su ba, daga baya suka kira ni suna cewa, in har ba zan bayar da kudi ba to ba za su zo su yi aikin daukar hoton wurin da aka yi kisan ba. Ganin irin wannan tashin hankalin da nake fuskanta sai na wuce wurin mai Unguwar mu daga na muka wuce wurin Dakacin yankin Malam Haruna Ahmed inda shima ya ce, tabbas iyayen yaran da suka yi kisan ne ya kamata su bayar da irin wannan kudaden, ya kuma bukaci in dan basu lokaci su yi nasu dabarbarin, in sun cimma matsaya za su nemi ni.
Da na dawo gida sai wani tunani ya zo mun, na ce bari in kira DPO din CSP Lateef Abiodun in binciki halin da ake ciki, da na kira shi na tambaye shi sai ya ce wai har yanzu basu kira ni ba? Baza bada kudi ba ko?.
Wannan lamarin ya tayar mani da hankali, musamman ganin yadda lamarin ya tamkar yawo da hankali, kusan duk lokacin da iyalina ta tuna kisan da aka yi wa danta suma take yi, har sai an kai ga sanya mata ruwa. Har zuwa yanzu babu wanda ya kira ya yi mani wani bayani na halin da ake ciki.
Ana kuma ta rade-radin cewa, iyayen daya daga cikin yaran sun sayar da gidansu a kan Naira Miliyan 2 sun kai wa ‘yansanda da sunan a kashe maganar, duk da dai ban tabbatar da labarin ba.
Matasa Sun Yunkuro Neman Daukar Fansa
Tun da aka yi kisan nake fama da abokansa da sauran matasan yankin don suna ta kokarin daukar fansa amma ni nike kwantar musu da hankali, ina cewa, mu bar komai tunda lamarin yana hannun ‘yansanda, yakamata kowa ya saurara har muga irin hukuncin da za a yi musu.
A tunani na dai har yanzu suna nan a hannun ‘yansanda a can ‘State CID a Minna.
Daga baya an bani shawarar in rubuta wa Kwamishinan ‘yansanda takardar tuni amma Dakaci ya ce in dan dakata tukuna shima zai yi nasa kokarin na neman sanoi halin da ke ciki. Zuwa yanzu kuma Dakacin bai yi magana ba ballantana har muje wajen DPO a rubuta takardar.
Kuma gashi bani da halin daukar lauya kamar yadda wasu mutane ke bani shawarar yi. Asalin sana’ar kanikancin manyan mota nake yi, daga baya na koma tuki, na yi aikin tuki da kamfanin Marigayi Shehu ‘Yaaduwa, a hali yanzu kuma ina tuka motar daukar ‘Block’ ne a garin Suleja. Ina bukatar al’umma su taimaka mani don kwato wa yaro na hakkinsa.
‘Yansanda Sun warware zare da abawa
Wakilinmu ya tutubi jami’in ‘yansanda na yankin, CSP Lateef Abiodun don jin menene zai ce game da zargin da Malam Adamu shu’aibu ya yi na mayar dashi tamkar ATM da ‘yansanda suka yi, suna karbar kudade a hannunsa ba tare da kuma ana samun cikakken cigaba ba a kan kokarin kwato wa yaronsa hakkinsa, inda ya bayyana cewa, a halin yanzu sun kammala nasu binciken sun kuma mika Kes din ga ofishinsu na CID da ke Minna don cigaba da bincike.
Ya ce tunda lamarin ya shafi kisa basu da hurumin rike kes a matakinsu. Don haka sun mika mutum biyu da ake zargi zuwa can. Ya ce, shi dai bai san batun karbar kudi daga hannun mahaifin yaron ba.
Haka kuma wakilin namu ya tuntubi Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansandan Jihar Neja, DSP Wasiu A. Abiodun ta wayar tafi-ga-gidanka inda bayyana cewa, sai ya samu cikakken bayani daga Jami’in da ke kula da Kes (IPO) din kafin ya iya yin cikakken sharhi, ‘Amma yakamata a fahinci cewa, a irin wannan halin, wanda aka yi wa kisa yana a matsayin mai kara ne (Complainant) don haka dole a nemi shi a dukkan matakan binciken da ake yi na gano yadda lamarin yaru, tun daga nan wajen ‘yansanda har zuwa kotu, saboda haka babu mamaki in har ‘yansanda sun nemi mahaifin yaron ya rinka zuwa daga lokaci zuwa lokaci, “Amma tabbas jami’anmu suna da cikakken horo da kwarewar gudanar da ayyukansu, ya kuma kamata a fahinci cewa, binciken abin da ya shafi kisa abu ne dake bukatar takatsantsan, dole a bi a hankali don a ba kowa hakkinsa” in ji shi.