Tun bayan hade farashin canjin Dala da Naira a kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi kwanakin baya, an samu karuwar shigowar kudade a kasuwanci shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashe waje.
Bincike ya nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yuni na wannan shekarar an samu karuwar hada-hadar da dala miliyan 270, kamar yadda kididdigar ta nuna.
- Cire Tallafin Mai: Za A Fara Bai Wa Talakawa Dubu 8 Duk Wata
- Cire Tallafin Mai: Za A Kara Farashin Burodi A Nijeriya
Wannan karuwar da aka samu ta faru ce tsakanin watanni biyu a jere, inda aka samu karuwar Dala biliyan 1.41 a watan Yuni koma bayan Dala biliyan 1.14 da aka samu a watan Mayu na shekarar 2023.
A farkon watan Yuni ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kudurin gwamnatinsa na hade yadda ake gudanar da safarar kudaden waje wuri daya a tsakanin bangaren gwamnati da kasuwannin bayan fage wanda hakan ya kawo karshen yadda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke gudanar da kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje cikin tsarin gwamnati.
Duk da cewa, masu zuba jari ba su fara shigowa Nijeriya ba tun bayan da aka fara wannan tsarin na sake kasuwar kudaden kasashen waje, musamman ganin wannan shi ne babban burin shirin, amma kididiga na baya-bayan nan tana nuna cewa an samu nasara da karuwar yadda dala ke yawo a kasar nan an kuma samu daidaita farashin dala a tsakanin ‘yan kasuwa da al’ummar Nijeriya.
Bayanai da aka samu daga ma’aikatar kudi ta Nijeriya na cewa, an samu karuwar shigar kudi daga kasashe waje da kashi 44.3 a wata wanda ya yi daidai da dala miliyan 298.8 a cikin watan da ake magana a kai, lamarin na kama da abin da ya faru a lokacin da aka fuskanci annobar cuta korona a shekarar 2019 inda aka samu dala biliyan 1.56, wannan na faruwa ne saboda yadda masu zuba jari ke yin dari-dari duk kuwa da yadda aka bude kofar cin kasuwar kudaden kasashen waje.
A wani bangaren kuma hada-hadar kudade na cikin gida sun karu daga kashi 19.3 cikin wata daya daidai da Dala biliyan 1.11 saboda yadda kudade da ke fitowa daga bangarorin da na bankuna suka matukar karu, ya kuma haura zuwa kashi 35.7 daidai da Dala 597.10. Haka kuma kudaden da aka sau na fita da kayayyaki ya karu daga kashi 2.3 zuwa Dala miliyan 448.00.
Masana a cibiyar binicike ta ‘Cordros Research’ sun yi imani da cewa, masu zuba jari za su dauki matakin zuba ido don lura da yadda Babban Bankin Nijeriya CBN zai gudanar da shirin da kuma lamarin zai gudanar don kada su shigo a samu matsala jarinsu ya rushe.
Masu sharhi sun kuma bayyana cewa, masu zuba jari daga kasashen waje suna fatan wannan tsarin zai samu nasara don haka masu zuba jari daga sassan duniya za su samu kwarin gwiwar shigowa Nijeriya don gudanar da harkokin kasuwancinsu ba tare da tsoro ba.
A kan hanyoyin da ake gudanar da shirin kuma, masana sun tabbatar da cewa, lallai ana kan hanyar samar da tsari mai kwari wanda ya yi daidai da abin da ake samu a sassan duniya. Sun ce akwai bukatar a tattabar da ana aiwatar da shi yadda kamata ba tare da wani tsoro ba.
Tsari na baya baya da aka fito da shi wanda ya sha banban da wannan ake amfani da shi a halin yanzu inda ake hadaka tsakanain masu zuba jari da Babban Banki shirin da ake amfani shi a halin yanzu yana bayar da karfi ne a kan yadda hada-hadar kasuwancin ke tafiya, shirin ya fara aiki ne daga ranar 5 ga watan Yuni na wananna shekarar 2023.
Masanan sun kuma jaddada cewa, in aka samu bunkasar yadda ake tattara bayanai aka kuma yi aiki tare da bayyana yadda ake gudanar da shirin ba tare da boye-boye ba tabbas hakan zai haifar da karuwar shigowar masu zuba jari na ciki da kasashe waje, wanda tabbas wannan zai kara bunkasa tattalin arzikin kasa mai dorewa.
A halin yanzu, a makon farko na watan Yuli 2023 farashin dala ya karye da Naira 19.20 ko kuma kashi 2.48 zuwa naira 792.20 a cikin mako biyu, wannan kuma sakamakon yadda masu zuba jari suka zuba ido a kan yadda bukatar al’umma na dalar a sassan Nijeriya ne.
A kasuwar shiga da fitar da hajojin Nijeriya, naira ta fadi da kashi 1.0 zuwa Naira 776.90 a kan dala daya inda zuwa ranar 6 ga watan Yuli aka yi asarar kashi 48.1 zuwa dala miliyan 367.23. A kasuwar shiga da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kuwa ana sayar da dala daya a kan naira 600 zuwa naira 820 a kan dala daya.
Masu lura da yadda aka gudanar da kasuwar kasashen waje a makon da ya gabata sun lura da yadda farashin naira ya yi tangadi a kan dala da kashi 4.74, kashi 4.59, kashi 4.47, kashi 4.14 da kuma kashi 3.64 inda aka sayar da dala a kan Naira 801.22, N810.72, N820.24, N849.13 da kuma N910.26 a watannin farko.
Haka kuma a kasuwar hada-hadar sayar da danyen man fetur, a ranar Juma’a kudin gangan man fetur ya kai dala 78.50, wannan kuma yana faruwa ne saboda yadda kasar Saudi Arebiya da kasar Rasha suka yanke shawarar rage adadin gangan man da suke hakowa.
Masana na fatan a nan gaba kadan farashi zai daidaita, za kuma a samu bunkasar kasuwanci a dukkan bangarorn tattalin arzikin kasa, in har ba a samu wani gaggarumin canji daga yadda aka tsara tafiyar da al’amurra ba.