Tun daga ranar 10 ga watan Afrilu, kasar Sin ta fara karbar karin harajin kwastam na kaso 84 bisa dari kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar daga kasar Amurka, domin mai da martani ga kasar Amurka ganin yadda take kara haraji kan kayayyakin da ake shigar da su kasar daga kasar Sin. Daga bisani kuma, kasar Amurka ta sanar da kara harajin kwastan zuwa kaso 125 bisa dari kan kayayyakin da ake shigar da su kasar daga kasar Sin. Sa’an nan, a ranar 10 ga wata bisa agogon kasar Amurka, farashin hannayen jari na manyan kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar guda 7 suka ragu, wadanda suka hada da kamfanonin Apple da Microsoft da sauransu.
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, kasar Amurka ta ci gaba da kara harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigar da su kasar daga kasashen ketare, bisa hujjar rage gibin ciniki, harkar da ta haddasa rudani cikin kasashen duniya, har ma a cikin gidan Amurka.
- 2027: Masu Shirin Yin Kawance Na Duba Yiwuwar Zakulo Dan Takarar Da Zai Yi Wa’adi Daya
- Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto
A bangaren kasar Sin kuwa, ana ci gaba da kare karkon tattalin arzikinta domin tabbatar da karko na kasashen duniya.
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda wajen kare karfin tattalin arziki da cinikayya.
Kwanan baya, manyan jami’an kasar Sin sun yi shawarwari da takwarorinsu na kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) da na kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda suka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga waje. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa mai ba da tabbaci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, idan aka kwatanta da kasar Amurka wadda ta sha fitar da manufofi na rashin hankali. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp