Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Matthew Dogara Daje a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a mazaɓar Munya ranar Asabar.
Daje ya samu kuri’u 12,556 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Sabo Sunday Adabyinlo na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 5,646.
Sakamakon da INEC ta fitar, APC ta samu nasara a unguwanni 10 yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta samu nasara a unguwa daya.













