Wani dan Majalisar Wakilai, Hon. Jafaru Mohammed Ali, ya yi ikirarin cewa ‘yan bindiga suna amfani da keɓeɓɓen dajin Kainji na ƙasa da ke Jihar Neja a matsayin babban sansaninsu inda daga nan suke kaddamar da muggan hare-hare kan kananan hukumomin Agwara da Borgu na Jihar; kananan hukumomin Bagudo da Shanga a Jihar Kebbi, Kaiama/Baruten a Jihar Kwara da wasu al’ummomi makwabta a Jamhuriyar Benin.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Borgu/Agwara ta Jihar Neja a Majalisar tarayya, wanda ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja ranar Laraba, ya bayyana cewa yawancin ‘yan bindigar bakin haure ne wadanda ba sa iya jin harsunan Nijeriya.
Dan majalisar ya yi kira ga Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, da ya tura sojoji tare da makamai na zamani domin share dajin na Kainji wanda a halin yanzu ‘yan bindigar sun mayar da dajin mafakarsu kuma wurin tarukansu.
Ya roki Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa da su samar da abinci da kayayyakin da ba na abinci ba ga wadanda suka tsira daga hare-haren ‘yan bindigar a mazaɓarsa.














