Dakarun rundunar hadin gwiwa ta MNJTF sun yi nasarar dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka kai a sansanin soji da ke Darak a kasar Kamaru, inda suka kashe ‘yan ta’adda 10.
Sanarwar da babban jami’in yada labaran soji na MNJTF, Lt.-Col. Olaniyi Osoba ya fitar, ta bayyana cewa, an kai musu harin ne da sanyin safiyar ranar 18 ga watan Disamba, 2024, inda ‘yan ta’addan suka kai farmaki daga wurare da dama a sansanin sojojin na Darak.
- Sojojin Chadi Sun Fatattaki ‘Yan Boko Haram Zuwa Kamaru Da Nijar Da Nijeriya
- ‘Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-19 Sun Kammala Ayyukansu Na Farko A Wajen Kumbo
Sai dai ya ce, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda suka harbe ‘yan ta’adda shida nan take tare da tilasta wa sauran guduwa da raunuka daban-daban na harbin bindiga.
Lt.-Kol. Osoba ya bayyana cewa, wasu sojoji biyar sun samu raunuka a yayin artabun wanda a halin yanzu ke samun kulawa a asibiti.
Sanarwar ta kara da cewa, a wani samame na bin baya da sojojin suka kai wa ‘yan ta’addan da suka tsere, a kauyen Mazogo da ke tsakanin Zamba da Djibirilli, an yi nasarar harbe hudu daga cikinsu tare da kwato kayayakin abinci na ‘yan ta’addan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp