Dakarun rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro, MNJTF a jihar Borno a karshen mako sun tarwatsa wasu gungun ‘yan ta’addan Boko Haram da ke kan hanyarsu ta kai wani mummunan hari a yankin Magumeri-Maiduguri.
A wata sanarwa da babban jami’in yada labaran soji na MNJTF, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar, ya ce, sojojin da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun kaddamar da harin kwanton bauna, inda suka kawar da barazanar kafin ‘yan ta’addan su yi barna a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
- Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Sun Kawar Da Fargabar Ɓallewar Madatsun Ruwa A Arewa
- Hare-haren ‘Yan Bindiga A Sahel Sun Jefa Shugabannin Soji Cikin Zulumi
Laftanar-Kanar Osoba ya ce, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan ne a lokacin da suke fitowa daga wani daji a kan babura.
Sanarwar ta ce, da ganin sojojin, ‘yan ta’addan sun yi yunkurin tserewa amma sai suka gamu da harbe-harbe ta ko’ina.
“Wannan bude wutar, ya tilasta musu barin makamansu da babura, lamarin da ya kawo cikas ga shirinsu na ta’addanci a yankin,” inji shi.