A yau Talata, mai magana da yawun rundunar sojojin kasar Sin ya bayyana cewa, dakarun rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin, watau PLA sun yi shirin ko-ta-kwana domin tinkarar duk wani matakin soji na tayar da zaune tsaye a tekun Kudancin Kasar Sin.
Kazalika, duk dai a yau din, dakarun sojin sama na rundunar ta PLA da ke shiyyar kudanci ta gudanar da shawagin sintiri a sararin samaniyar kasar Sin ta tsibirin Huangyan. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)