Dakarun ‘Operation Forest Sanity’ a ranar Juma’a sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da kubutar da wasu mutane uku a Ungwan Madaki da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da afkuwar lamarin a wani martani da jami’an tsaro suka bayar biyo bayan aiki da suka yi daga yankin.
- Yadda Tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya Suka Habaka Noma A Nijeriya
- Sashin Blue Line Na Layin Dogo A Legas Ya Zama Wani Muhimmin Aikin Dake Shaida Hadin-Gwiwar Sin Da Najeriya
Aruwan ya ci gaba da bayanin cewa, a cewar rahoton jami’an tsaro, sojojin sun isa yankin inda suka yi artabu da ‘yan ta’addar, lamarin da ya tilasta musu tserewa suka bar wadanda suka sace.
“Sojoji sun ceto mutane uku: Elkanah Eli, tare da ‘yarsa, da kuma Mista Yahaya,” in ji shi.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta gode tare da yaba wa sojojin bisa bajinta da nasarar da suka yi wajen ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma kara da cewa, “an sake hada su da ‘yan uwansu.