Dakataccen Malamin Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Captain Elechi Amadi Polytechnic da ke Fatakwal a jihar Ribas, Mista Zoe Solomon Tamunotonye, ya koma karen mota domin neman taro da sisin da zai ciyar da kansa biyo bayan kin biyansa albashinsa na sama da watanni shida da Kwalejin ta ki yi.
A wani faifan bindiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, an ga Tamunotonye na gwagwarmayar neman fasinjoji da su shiga motar kabu-kabu a kan hanyar Ikwerre da ke garin Fatakwal babban birnin jihar Ribas.
Shi dai malamin kwalejin, hukumar gudanarwar ta Kwalejin ce ta dakatar da shi biyo bayan rahoton da kwamitin da aka kafa domin bincikensa kan zargin lalata da wata dalibar Kwalejin.
Tirka-tirkar alakar da ke tsakaninsa da dalibar har sai da ta kai ga ‘yan sanda sun tsare ita dalibar a caji ofis din Sani Abacha da ke garin na Fatakwal.
Malamin ya dawo ya zargi dalibar da karkatar da kudin da ya kai naira N250,000 da ya bata domin yin kasuwanci kuma ta rike masa makullin ofis da wasu kadarorinsa.
Daga baya ne kuma kwamishinan ‘yan sanda Eboka Friday ya shiga cikin lamarin da har aka sake dalibar bisa cewa bayan da ya saurari dukkanin bangarorin da abun ya shafa, ya gano zargin da malamin ke yi babu sahihin gaskiya a ciki.
Idan za a iya tunawa dai Kwalejin ta Captain Elechi Amadi Polytechnic a watan Maris na 2022 ta fitar da sanarwar na cewa ta samu Zoe Solomon Tamunotonye dumu-dumu kan zarginsa da ake yi da rashin da’a gami da cin zarafin dalibar.
Sanarwar wacce Rijistan Kwalejin Chris Woke ya sanya wa hannu inda suka bai wa malamin Kwalejin zuwa ranar 31 ga watan Mayun 2022 da ya rubuta wasikar neman afuwa da yafiyar Kwalejin tare da daukan alkawarin zai zama daga cikin malamai masu cikakken da’a da ladabi.
Sai dai Malamin ( Zoe Solomon) ya ki rubuta neman yafiyar bisa nashi ra’ayin na cewa shi fa atafau bai aikata laifin komai da zai sanya shi rubuta ban hakuri da neman gafara ba.