• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalibai Miliyan 1.4 Da Suka Rubuta Jarra-bawar UTME Sun Ci Maki Kasa Da 200

bySulaiman and Khalid Idris Doya
1 year ago
UTME

Hukumar shirya jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu a kasar nan (JAMB), a ranar Litinin da ta gabata ta sake sakamakon jarabawar na shekarar 2024, inda sakamakon ya nuna cewa dalibai 1,402,490 daga cikin 1,842,464 sun kasa iya cin maki 200 daga cikin maki 400 na jarabawar.

Adadin daliban da suka kasa cin sakamakon sun dauki kaso 78 cikin dari na duk-kanin daliban da suka zauna domin rubuta jarabawar kamar yadda sakamakon da JAMB ta fitar ya nuna.

  • JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
  • UTME: JAMB Ta Ba Da Umurnin Kamo Iyayen Da Aka Gansu Kusa Da Cibiyoyin Zana Jarabawa

Da yake bayar da bayani kan sakamakon jarabawar dalibai 1,842,464, Rajistara na hukumar, Farfesa Ishak Oloyede, ya ce, “Dalibai 8,401 ne kawai suka iya samun maki 300 ko fiye da haka, dalibai 77,070 sun ci maki 250 ko fiye, sai kuma 439,974 da suka ci maki 200 ko fiye, yayin da kuma dalibai 1,402,490 suka ci maki kasa da 200.”

Ya ce, hukumar ba ta saba wallafa sunayen wadanda suka yi zarra a jarabawar ba, illa iyaka tana fito da jerin yadda sakamakon ya kaya.

A gefe guda, shugaban hukumar ya nemi al’umma da ka da su sake fadawa irin tarkon da Mmesoma ta taba jefa wasu, inda ya ce a kowani lokaci wani ko wata daliba suka yi ikirarin samun wasu sakamakon jarabawar mai gwabi, kafin mutane su dukufa wajen musu kyautuka su nemi tabbaci daga hukumar domin kauje wa shiga kokonto.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Oloyede ya kuma ce an rike sakamakon jarabawar dalibai 64,624 daga cikin wadanda suka zana jarabawar, inda ake kan gudanar da bincike kan zargin satan amsa, sahihancin cibiyar zana jarabarsu da dai sauransu.

A cewarsa, adadin daliban da suka yi rajistan zana jarabawar sun kai 1,989,668, inda a cikin dalibai 80,810 ba su je sun zana jarabawar ba, “Adadin dalibai 1,904,189 ne suka zauna domin zana jarabar UTME a cikin kwanaki shida.”

Oloyede ya ce hukumar ta shirya wa daliban da suke kasashen waje jarabawa a wurare tara da suka hada da Abidjan, Ibory Coast; Addis Ababa, Ethiopia; Buea, Cameroon; Cotonou, jamhuriyyar Benin; London, Burtaniya; Jeddah, Saudi Ara-bia; da Johannesburg, Afrika ta Kudu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Next Post
Goro

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version