Dalibai sama da 300 a cibiyar koyar da Sana’o’i ta zamani ta Dangote, sun yi zanga-zangar bore na nuna damuwa kan korarsu da cibiyar tayi.
Daliban, sun yi gangamin ne a fadar sarki da gwamnatin jihar Kano, inda suka bayyana cewa, korar an yi ta ne ba bisa ka’ida ba, kuma sun zargi wani mahukunci, Paul Quin a cibiyar da sa hannu a korar su.
Zanga-zangar, karkashin jagorancin daya daga cikin daliban da aka kora, Abubakar Isma’il D.Turawa ya nemi hukumomin da abin ya shafa da su sa baki domin mayar da su cibiyar.
“Muna rokon gwamnati da ta sa baki ta dawo da mu cibiyar mu domin mu kammala horon da a ke mana da kuma amfana daga dukkan shirye-shiryen da aka shirya mana,” in ji shi.
Kokarin tattaunawa da Daraktan ya ci tura domin bai amsa kiran nasa ba ko kuma amsa sakon da aka aika masa. Rahoton Daily Nigerian Hausa.