Wani dalibin Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Kashere (FUK) a Jihar Gombe, mai suna Nalkur Zwalnan Lar, da ke matakin karatu na 400, ya rataye kansa har lahira a wajen makarantar.
Kamar yadda majiyoyi suka shaida wa LEADERSHIP, marigayin ya kashe kansa da kansa ne a rukunin gidaje na Santuraki a kusa da sandar layin sadarwa (mast).
- Sin Tana Bayar Da Damar Hadin Gwiwa Ta Hanyar Ayyukan Binciken Duniyar Wata Na Chang’e
- Zaben Kananan Hukumomin Osun Haramtacce Ne – Kotu
An gano cewa, Lar ya kashe kansa ne bayan da dawowa harkokin karatu da aka yi biyo bayan janye yajin aikin ASUU, inda ya fahimci cewa budurwarsa ta auri wani na daban a hutun yajin aikin kusan wata takwas da ASUU ta shafe.
Bayan wannan, daga cikin dalilin da ya kaisa ga yin bankwana da duniya har da cewa ya kasa iya sayen wayar zamani a kan kudi N50, 000 duk da zargin da yayi na cewa mahaifinsa na da miliyoyin Naira.
A cewar makwabtansa da suka samo wasikar bankwana da duniya da marigayin ya rubuta, Lar ya misalta cewa bai cancanci ci gaba da rayuwa a wannan duniyar ba tun da ba zai iya mallakar wayar Naira N50, 000 yayin da mahaifinsa mai kudin gaske ne.
Sun kuma ce ya nuna bacin ransa da damuwarsa bisa yadda budurwarsa ta je ta auri wani ba tare da saninsa ba, ya ce ta ci amanarsa ta yaudareshi, kuma rashin samun kudaden daga wajen mahaifinsa ya kara fusatashi ga daukan wannan matakin hallaka kai.
Sannan, sun ce dalibin ya rokesu da kada su bude wasikar da ya rubuta har sai bayan mintina 20 da basu daga baya ya ce su kai wa iyayensa wasikar.