1.Tsarin koyarwa yana nuna dalilin da ya sa za a koyar da maudu’in ko darasin. Ta haka ne dalibai za su koma gida da fahimtar abinda aka koya masu, a aji.
Rubuta ko hanyoyin da za a koyar shi ne abu na gaba. Anan Malami zai yi bayani kan dabarun da za su taimaka wa dalibai su gane darasin da aka koya masu.
- Kidayar Jama’a Da Harkar Ilimi
- Gwamna Uba Sani Zai Kaddamar Da Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ungozoma A PambeguaÂ
A matsayinka na Malamai kana iya amfani da abubuwan da suka faru matsayin misalai na hakikani a rayuwa, tare da abubuwan da na iya kasancewa a matsayin mutum na ji, ko ganin abin tamkar ya auku ne.Wannan zai sa dalibai su sa zurfin tunaninsu har su gane dalilin ko gane abin da ake koyar da su.
Bayan an bayyana dalilan da suka sa za koyar da hanyoyin da za ayi amfani da su, sai ka yi aiki ta yadda za ka iya auna ko gane wacce irin fahimta su dalibai suka yi ma darasin da ka kya masu.
Anan ko nan ya dace ka dogara kan irin ayyukan da akake basu(a baka ko kuma rubuce a matsayin matakan da zaka yi amfani da su wajen gane fahimtarsu kan darasin da ka koya masu.Za ‘a shirya lokacin da za’a yi tambaya da amsa tare da shirya abubuwan da zasu taimaka maka gane hazakar dalibanka kan abubuwan da kake koya masu.
2.Shirya yadda za ka yi amfani da lokaci a cikin azuzuwa
Tsarin koyarwa na bi da bi zai taimakeka wajen koyar da muhimman sassan darasin a cikin lokacin da ka ware ma lokacin koyarwa.
Kada ka sa kanka cikin damuwa har ma ka rasa yadda za ka amsa tambayar da dalibi ya yi maka. Idan har ka lura kwarai da gaske tunda yake kana da dukkan abubuwan da suke dace a hannunka, za ka koyar cikin nasara ba tare da ka rasa yadda zaka yi ba.
3.Tsarin yadda za a koyar zai mai da ko sa Malamai su zama da, ka gan su ba zaka ga wata razana ba tare da shi ko su ba.
Idan kana da tsarin yadda za a koyar tare da kai, sai ka kasance Malamin da bai da wata damuwa. Ka kasance kowane lokaci kana da dabaru da tsarin koyarwa wadanda ake amfani dasu yanzu.
Ba zaka dogara da hanyoyin koyarwa irin na shekarun baya ba,amma sai hanyoyin da za su nuna maka sabbin dabaru na koyarwa. Shi tsarin koyarwa yana taimaka maka maida hankalin ka, kan wadanda suka kasance nagartattu ne.
Idan har ka yi amfani da wannan sai ka zama Malami wanda bai da kasala ko tsoron yadda zai fuskanci daliban shi a mizanin wanda ya san abinda yake koyarwa.
- Wata hanya mai sauki ce ta koyarwa yadda za’a gane
Abinda za a koyar da yadda za a koyar tambayoyi biyu ne da suke bukatar amsoshi daga Malamai.
Idan ko matukar ka san darussan da zaka koyar da kuma yadda za a koyar da su, ba zaka samu wata matsala ba wajen dabarun koyarwar ka, da za su ilimantar da dalibanka.
Akwai abu daya da zaka tuna da shi!
Idan zaka koyar daga bangon littafi zuwa karshen shi wannan ba yana nufin ka cimma burin koyarwa nagartattu ba.
Tsarin koyarwa yana yin nuni kan darussan da suka kamata ba wadanda suka zama babu lalle ba dole.