Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta shirya tsaf don kaddamar da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke karamar hukumar Soba a yankin Zaria da ke Jihar.
Hakan na kunshe ne acikin wata tattaunawa da manema labarai da shugaban kwalejin, Dakta Yusuf Bello ya yi ranar Litinin, 9 ga watan Satumba, 2024 gabanin kaddamar da Kwalejin a harabar Kwalejin da ke Pambegua.
- Gine-gine Da Zubar Da Shara A Magudanun Ruwa Ke Haifar Da Ambaliya A Kaduna – Kwamiti
- Zanga-zanga: Gwamna Uba Sani Ya Musanta Sanya Dokar Hana Fita A Kaduna
Kwalejin Ta Pambegua, daya ce daga cikin sansanonin kwalejojin da ke da babban sansani a Asibitin Dantshoho, a birnin Kaduna, karkashin shugabancin Dakta Yusuf Bello.
Sansanonin Kwalejin sun hada da Kwalejin Koyon aikin jinya ta Asibitin Dantsoho, Tudun wada, da ke cikin birnin Kaduna; Kwalejin Koyon aikin jinya, Kafanchan, da ke kudancin Kaduna, da Kwalejin Koyon aikin jinya, Pambegua da ke yankin Zaria.
Kwalejin ta samu amincewar hukumomin da ke kula da manyan makarantun kiwon lafiya, da hukumar kula da manyan makarantun kimiyya da fasaha (NBTE) don gudanar da karatuttuka a bangaren aikin jinya na shekaru hudu a jere (ND-HND Nursing), ungozoma (Basic Midwifery) da General Nursing.
Dakta Bello ya jinjina wa al’ummar Pambegua bisa namijin kokarinsu da aljihunsu, da karfinsu wajen ganin an samu damar kaddamar da wannan kwalejin a yankinsu, har ta kuma fara aiki.
Shugaban ya kuma sake mika godiyarsa ta musamman ga Gwamna Uba Sani kan kishinsa ga ci gaban al’ummar Kaduna baki daya.
Tun da farko, Hakimin Pambegua, Karfen Dawakin Zazzau, Sufyan Sani Usman, ya jinjina wa Gwamna Uba, bisa kafa irin wannan kwalejin a yankin, inda ya ce, kwalejin ba al’ummar Pambegua kadai ce za ta amfanar ba, har da yankin Zaria da Jihar Kaduna baki daya.
Hakimin ya kuma gode wa Dakta Bello Yusuf wajen ganin wannan Kwalejin ta samu nasarar kafuwa.
Shugaban kwamitin kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Pambegua, Alhaji Haruna Ahmad, ya kuma yaba da irin gudunmawar da al’umma suka bayar, da suka hada da gyare-gyare da kuma sayan kayan aiki domin tabbatar da gudanar da ayyuka a kwalejin.
Ya kuma yabawa gwamnati bisa yadda ta tabbatar da aikin da aka dade ana jira a yankin tare da tabbatar da cewa al’ummar karkara za su ci gajiyar kokarin gwamnati.
Shi ma Akanta Janar na Jihar Kaduna, kuma tsohon shugaban karamar hukuma, Alhaji Bashir Suleiman Zuntu, ya yaba da irin nasarorin da gwamnati ta samu, ya kuma yi fatan samun nasarar gudanar da ayyuka a kwalejin ta Pambegua.
Talla