Ci gaba daga makon da ya gabata
3-Rashin Tsara Lokaci
“Lokaci kudi ne,”mutane na yawan fadar haka.Gaskiyar lamarin shi ne ba a san yadda za ayi amfani da lokaci ba domin cimma wani buri,shi ya sa idan dalibi bai san muhimmancin lokaci ba wannan ya nuna kamar kudi ba a san darajarsu ba.
Haka wadannan lamuran suke a jarrabawa saboda yawancin dalibai suna bari ne har sai Malami ya ce a kawo ma shi aikin da ya bada zai duba ko yin gyara lokacin ne zasu yi kokarin farawa wanda a lokacin suna da wasu ayyukan da suka shige masu gaba.
Barin yin Nazari ko karatu sai wani lokaci irin haka ne ke kawo rashin shiryawa jarabawa kamar yadda ya kamata su yi.
Mafita:
Ka yi kokari ka yi aikin ka lokacin da Malami ya bada ba sai lokaci ya kure ba, kamata ya yi a ware lokaci na yin karatu da sauran abubuwa,yin haka zai taimakawa kai mai karatu yin amfani da lokacin ka,ba tare da wani bata lokaci ba.
Dabi’ar karatu da bata dace ba
Da akwai wasu daliba wadanda su sam ma ba su bukatar karanta littattafai saboda su ragaye ne,abin ba haka bane saboda su suna yin karatu ne lokacin da bai kamata ba, hakanan ma yin barci lokacin da ya dace ace suna yin karatu.
Iyaye na matsa masu su yi barci da sauri amma su basu matsawa kansu su tashi da wuri ba,su karanta wasu littattafai, wannan ya nuna sun fi bukatar su yi barci na lokaci mai tsawo,su yi tunanin yin karatun littattafai da dare.
Da dare lokaci ne na yin barci shi yasa idandalibai suka so yin karatu da dare sai barci ya kama su.Dalili shine da dare ragwanci ya fi kama dalibai.
Mafita:
A yi kokari a tashi da wuri domin a fara karatu dalibi ya dace yam aida hakan halayyar shi a rika yin hakan kullun.A tilastawa kai a karanta littattafai masu yawa da rana kafin lokacin shiga aji.
5 Rashin amincewa da kai
“Idan kana ganin za kayi nasara to za kayi idan kuma kana ganin ba nasara tare da kai to ba za ka yi nasarar ba”.Mutanen da suke ganin ba za su iya cin jarrabawa ba sna faduwa ba tare da wani rashin tabbas ba.Hakan ta kasance domin ba su son su yi nasara.
Mafita
Koda wane lokaci ka rika Kallon kana iya cin jarabawa idan hakan tana kasancewa watarana sai labari domin kuwa kana iya samun nasara a jarrabawa.
6 Kunci da fatara
Wanda bai ta shi cikin wadata ta kudi ba bai da wani tabbas cewar zai iya zama wani a rayuwa,alal misali dalibi wanda yake fuskantar matsalar rashin kudi za iyi wuya ya samu damar sayan kayan karatu wadanda suka kamata.Duka bin da za su yi shi ne samun wata matsaya mara tsada, irin hakan shi yasa suke haduwa da rashin nasara.
Mafita
Sai ayi kokari a samu aikin wucin gadi sannu sai a samu wanda zai iya wadatarwa domin hakan zai taimaka.
7 Sa kai cikin al’amura daban-daban
Sa kai cikin abubuwa daban- daban na iya shafar karatu ko shirin fuskantar jarrabawa saboda shi wanda abin ya shafa bai da lokacin da zai bar jiki da kwakwalwarsa su huta.
Lokacin da kwakwalwa da jiki suka gaji suna son wanda ya mallake su ya yi barci ko kuma ya yi wani abu amma ba karatu ba, kamar dai yadda aka yi magana tun farko ita maganar ragontaka shi ne muhimmin abin da ke sanadiyar dalibai suna faduwar jarabawa.