Ga duk wanda ya ke sha’awar wasanni musamman ƙwallon ƙafa a Kano,ya shaida yadda Kano Pillars suka nuna Kapaciti da izza a yankin arewa har suka shiga cikin ɗaya ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafi daraja a Nijeriya. Amma yanzu, wannan babbar ƙungiya na cikin halin koma baya mafi muni, duk da tana ƙoƙarin dawo da martabarta amma har yanzu abin ya ci tura.
Ga masu bibiyar ƙungiyar tsawon shekaru, wannan koma baya nanmatukar sosa zuciya, domin Pillars ba kawai ƙungiya ba ce; wata alama ce ta alfaharin Kano da ruhin wasan ƙwallon kafa a birnin.
- Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
- Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna
Shekaru da dama, Kano Pillars sun kasance alamar ƙarfin iko da kwarewa a ƙwallon ƙafa a arewacin Nijeriya. Amma kakar 2024/25 ta zama ɗaya daga cikin mafi duhu a tarihin ƙungiyar, sakamakon ɗaukar ‘yan wasa marasa kyau, da ƙarancin amfani da damar da aka samu na zura kwallo, da tsoma baki ko katsalandan, da kuma tarzoma daga magoya baya.
Duk da samun cikakken tallafi na kudi da walwala daga Gwamnatin Jihar Kano, ƙungiyar ta gaza juya wannan tallafi zuwa nasara a filin wasa.
Zan yi duba tare da sharhin wadannan matsaloli don watakila a samu masu ruwa da tsaki su don daukar mataki, kuma masu sha’awar wasanni da magoya bayan kungiyar su san yadda aka haihu a ragaya.
1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo
Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba.
Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa ya cimmasa.
2. Tallafin Gwamnati — Jin Dadi Ba Tare da Tasiri Ba
Ba kamar mafi yawan ƙungiyoyi a gasar NPFL ba, Pillars suna samun cikakken tallafi na kudi da walwala da duk goyon bayan da suke bukata daga Gwamnatin Jihar Kano. Albashi da ƙarin lada (bonus) suna samu a kai a kai, kuma wuraren horonsu yana ɗaya daga cikin mafi kyau a arewacin Nijeriya. Sai dai jin dadi ya gaza nunawa a cikin fili.
Samun jin daɗi ga kuma rashin nasara ya nuna cewa motsa sha’awa a ƙwallon ƙafa ba kawai maganar kudi ce ba, yana bukatar babban buri daga kungiya da yan wasa, da hangen nesa, da sha’awar yin nasara a aikace. Wasu ‘yan wasan ba su da yunwar kafa wani sabon tarihi, ba su da babban burin samun wata dama ko nuna kansu ko kuma fito da sunansu.
3. Tsoma Baki a Shugabanci
Wani muhimmin dalili da ya cefa ƙungiyar cikin wannan mummunan hali shi ne tsoma baki a shugabanci da yadda ake tafiyar da kungiyar. Wasu bayanai sun nuna cewa ana matsa lamba ga masu horarwa kan zaɓin ‘yan wasa, ko salon dabarun shiga fili a taka leda, da yayin sayen ‘yan wasa.
Wannan tsoma bakin yana rage amincewa daga magoya baya sosai, yana haifar da rikici na zaman doya da manja tsakanin yan wasan da wasu mahukunta, kuma yana hana masu horarwa aiwatar da amfani da dabarun da zasu iya kai wa ga nasara.
Ci gaba na gaske zai zo ne kawai idan kowa ya janye hannu ya bar ƙungiyar da masu horarwa su ɗauki cikakken hukunci da alhakin duk wani sakamako da ya biyo baya na nasara ko akasaninta.
4. Matsalar Gane Dabarun Ƙungiya
Idan aka kalli Pillars a yau, yana da wahala a iya bayyana wane dabaru su suke amfani da shi. Shin ƙungiya ce mai matsawa gaba-gaba (attacking)? Ko suna jiran dama don kai hari (counter attack)? Ko ƙungiya ce mai riƙe kwallo kamar Manchester city ko Barcelona?
Gaskiyar ita ce, suna haɗa komai amma ba ko yaushe ne ake iya ƙwarewa a komai ba. A yanzu sun haɗa komai ba tare da ƙwarewa a ko ɗaya ba.
Ta hanyar dogaro da wasannin baya na salon da suke amfani da shi na amfani da gefe da kuma yawan aika dogayen ƙwallo ta sama ya sa abokan taka leda sun gane Pillars Cikin sauƙi, musamman idan ana wasa da ƙungiyoyin da suke rufe gida sosai. Don dawo da martaba, ƙungiyar ana buƙatar sabunta dabaru da koyon saurin sauya salo idan wata dabara ta gaza aiki.
5. Matsin Lamba Daga Magoya Baya Da Koyon Sarrafa Fushi
Kano Pillars suna da magoya baya mafi ƙarfi a Nijeriya. Amma ƙauna na iya sauyawa zuwa matsin lamba. Wasannin gida a filin Sani Abacha, wanda a da ya kasance tsani mai tsoro gare su, amma a yanzu sun kasance da damuwa ga ‘yan wasa da ke tsoron fushin magoya baya a kowane wasan da suka yi rashin nasara.
Sarrafa tsammanin magoya baya ta hanyar magana a fili da nuna cewa nasara da rashin duk wani fanni na rayuwa da kuma a wasanni na da mahimmanci wajen dawo da ƙwarin gwuiwar masu kallo da kuma ɗakin sauya kaya.
A rubutu na biyu nazarina ya zurfafa cikin matsalolin tsarin fasalin ƙungiyar, al’adu, da wasu abubuwan ke hana ƙungiyar ci gaba tun daga damuwa kan lafiyar ‘yan wasa fargabar zuwan Azumin da ƙarancin ‘yan wasa a wasu sassan, da rashin tabbas na shugabanci, da buƙatar gaggawa yin hangen nesa don samar da ci gaba mai ɗorewa.














