Biyo bayan hadakar da Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya yi na shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) da kuma Cibiyar Binciken Harkokin Abinci ta Duniya (IFPRI), sun kaddamar da wani sabon rahoto.
Rahoton ya bukaci a rungumi fasahar kimiyya da kuma mayar da hankali a fannin zuba hannun jari, domin a bunkasa tsarin samar da abinci a Arewacin Nijeriya da kuma kara habaka fannin aikin noma.
Taken shi ne, yin amfani da fasahar zamani don lalubo mafita kan kalubalen da fannin aikin noma ke fuskanta a yankin.
An gabatar da wannan rahoton ne a babban taron bunkasa tattalin arzikin yankin da aka gudanar a Abuja.
Kazalika, rahoton ya zayyano wasu tsare-tsare da kuma dabarun da za a dauka a bangaren zuba hannun jari, musamman domin farfado da fannin aikin noma, duba da yadda Arewacin kasar ya jima yana fama da yawan rikice-rikice.
A jawabinsa a wajen taron, Babban Ministan Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ya sanar da wasu shirye-shiyen gwamnatin tarayya da suka hada da sauya wa rumbunan adana amfanin gona kashi 80 zuwa kusa da yankunan da kananan manoma suke a kasar.
“Muna kan yin aiki, domin ganin tabbatar da cewa; mun rage kalubalen karancin rumbunan na adana amfanin gona a Nijeriya,“ in ji Kyari.
Shi ma, a na sa jawabin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya jaddada muhimmancin shigowar kamfanoni masu zaman kansu cikin fannin, musamman domin samar tsarin aikin noma a fadin kasar mai dorewa.
“Hanya daya tilo da ta dace ita ce, ganin an magance talauci a Arewacin Nijeriya, wannan shi ne ta hanyar zuba hannun jari a fannin, musamman wajen yin noma; domin samun riba,” in ji Sarkin.
Shi kuwa a nasa jawabin, Dakaranta Janar na Bankin AfDB a kasar nan Abdul Kamara, ya jaddada cewa; habaka fannin yin noma domin samun riba a yankin, ta haka ne yankin zai iya cimma burin da ya sanya a gaba na bunkasa fannin aikin noma da kuma dorewar tattalin arzikin yankin.