Watannin goyon ciki, musamman daga zango na biyu zuwa na uku, lokaci ne da masu juna biyu suka fi fuskantar ciwon baya ko ciwon kugu.
Daga cikin dalilan ciwon baya ko ciwon kugu ko kuma na kwankwaso yayin goyon ciki, akwai sauye-sauyen da suke faruwa a kashin baya da kugu sakamakon karuwar nauyin ciki da kuma sinadaran haihuwa.
Hakan yana haifar da karuwar lankwasar kashin, sauyawar gurbin cibiyar nauyin jiki tare kuma da juyawar kugu ko kwankwaso.
Bayan wannan ya faru, sai ciwon baya da ciwon kugu su biyo baya har zuwa lokacin haihuwa. A wasu lokutan ma, ciwon yana ci gaba da wanzuwa ne har bayan haihuwa.
Sai dai, akwai hadarin gaske ga mai juna biyu ta yi amfani da kwayoyin ciwon baya barkatai, domin yin hakan na iya zama barazana ga lafiyarta da kuma abin da ke cikin cikinta.
Yana daga cikin muradan likitan fisiyo, sama wa mai juna biyu sauki daga ciwon baya da ciwon kugu ba tare da shan kwayoyin rage ciwo ba.
Ganin likitan fisiyo yayin goyon ciki, na da matukar alfanun kiyaye ciwon baya, karfafa yunkuri yayin nakuda da kuma kauce wa ciwon baya ko ciwon kugu, yayin da kuma bayan haihuwa.
Muna addu’ar Allah ya sauki masu juna biyu lafiya, wadanda ba su samu ba kuma su ma Allah ya ba su, amin summa amin.