Biyo bayan fashewar wasu manyan Bututun danyen Mai da ke a kasar nan da ke a yankin Bodo a jihar Ribas, wanda ake aikin tura man zuwa Nijar wato (TNP), hakan ya sanya, an samu raguwar man da ke sarrafawa.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a daren ranar Litinin data gabata ne, lamarin ya auku, wanda lamarin ya haifar da fargabar yuwar samun raguwar danyen Man da kasar ke hakowa.
- Kantoman Ribas Ya Naɗa Farfesa Lucky Worika A Matsayin Sakataren Gwamnati
- Kantoman Ribas Ya Dakatar Da Dukkanin Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa
Batutun Man na da karfin da zai tura danyen Man da ya kai sama da Ganga 450,000 a kullum.
Sai dai ba a san musababin abin da ya sanya fashewar manyan Bututun danyen Mab ba.
Amma wasu bayanai sun sanar da cewa, akwai batun yin zagon kasa ko kuma lalacewar da wasu Bututun Man suka yi da kuma barazanar da wasu ‘yan tayar da kayar baya suke yiwa Gwamnatin jaihar Ribas.
Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta.
danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun 2025, wanda ya kai yawan Ganga 1,465,006 da ake hakowa a kullum.
A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp