A daren ranar Asabar aka shirya buga wasan mako na 27 na gasar Laliga tsakanin kungiyoyin Fc Barcelona da Osasuna a filin wasa na Luis Companys da ke birnin Barcelona.
Amma sai aka samu labarin cewa mahukuntan gasar sun dakatar da buga wasan wanda aka shirya yi misalin karfe 9 na dare agogon Nijeriya.
- Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila?
- Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa
Daga baya kuma aka samu labarin cewar abinda ya janyo dakatar da wasan shi ne, mutuwar babban jami’in lafiya na Fc Barcelona Carles Minnaro Garcia wanda ya rasa ransa a daren ranar Asabar din.
Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp