ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa

by Sulaiman
1 year ago
Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya za ta yi amfani da damar da ta samu ta halartar Taron Kasuwanci na Faransa da ke tafe a birnin Paris don bayyana irin cigaban tattalin arzikin da aka samu ƙarƙashin shugabancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, a cewar Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris.

Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da ya karɓi gayyata zuwa taron daga Jakaden Faransa a Nijeriya, Mista Marc Fonbaustier, a lokacin wata ziyarar ban-girma da ya kai ofishin sa.

ADVERTISEMENT
  • Adadin Mata Mamallaka Sana’o’i Na Ta Karuwa A Kasar Sin
  • Abubuwan Sha Domin Karin Ni’ima Ga Mata

Idris ya jaddada cewa shirin gyaran tattalin arziki na Shugaban Ƙasa Tinubu yana haifar da sakamako mai kyau, yana mai misalta da daidaita darajar Naira da kuma raguwa a farashin abinci a matsayin alamun cigaban da aka samu.

LABARAI MASU NASABA

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara.

“Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara. Farashin abinci da ya hauhawa a baya yana sauka.

“Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.”

Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da ke aiwatar da sauye-sauye na tattalin arziki da zamantakewa tana fuskantar ƙalubale, amma ya jaddada cewa tsare-tsaren Shugaban Ƙasa Tinubu sun taimaka wajen rage wahalar da ke tattare da irin waɗannan sauye-sauye.

Ya ce: “Kowace ƙasa da ta aiwatar da wani sauyi na zamantakewa da tattalin arziki tana fuskantar matsaloli a farkon tafiya, amma ina ganin cewa a Nijeriya, an rage tsawon wannan lokaci saboda hangen nesa, jajircewa, da ƙarfin gwiwar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke da shi cewa wannan gyara zai kai Nijeriya ga ci gaba mai ɗorewa.”

Idris ya bayyana Faransa a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗar Nijeriya kuma ya buƙaci gwamnatin Faransa da ta mara wa shirin gyaran tattalin arzikin Tinubu baya domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

Har ila yau, ya jinjina wa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, bisa girmamawar da ya yi wa Shugaban Ƙasa Tinubu ta gayyata zuwa ziyarar gwamnati a watan Nuwamba 2024, yana mai cewa irin wannan girmamawa ba kasafai ake yi wa shugabanni ita ba.

Ministan ya tabbatar wa jakaden na Faransa cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiwatar da duk yarjejeniyoyin da ta ƙulla da gwamnatin Faransa a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu.

Haka kuma, Idris ya yaba wa Jakada Fonbaustier bisa ƙoƙarin sa na inganta hulɗar Nijeriya da Faransa tun daga lokacin da aka naɗa shi.

A nasa jawabin, Jakada Fonbaustier ya ce ziyarar sa ta ƙunshi ƙirƙirar hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da Shugabannin ƙasashen biyu suka cimma a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu a Faransa a bara.

Ya bayyana ƙudirin gwamnatin Faransa na tallafa wa Nijeriya wajen inganta hanyoyin sadarwa da fasahar yaɗa labarai.

Ya ce: “Dole ne mu tabbatar da cewa an yi aiki tuƙuru don bin diddigin ziyarar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a birnin Paris a watan Nuwamba.

“Shugabannin biyu sun tsara wata sabuwar hanya mai faɗi don haɓaka dangantaka, kuma a wannan fanni, sadarwa da watsa labarai suna da matuƙar muhimmanci.

‘A nan ne Faransa za ta iya bayar da gudunmawa ta fuskar ƙwarewa da fasaha.”

Jakaden ya bayyana Minista Idris a matsayin gwarzon sauyi a fannin sadarwa a Nijeriya, yana mai cewa matsayin sa a gwamnatin Tinubu ya dace da inganta matsayin Nijeriya a idon duniya da kuma janyo hannun jari daga ‘yan kasuwar Faransa da za su hallara a Paris a ranar 10 ga Afrilu, 2025, don Taron Kasuwanci na Faransa.

Nijeriya
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya
  • Sulaiman
    Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari
  • Sulaiman
    Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana
  • Sulaiman
    Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

MASU ALAKA

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF
Rahotonni

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin
Rahotonni

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026
Labarai

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
Next Post
Hadin Kai Ne Kadai Zai Kai Masana’antar Kannywood Tudun Mun Tsira -Ado Ahmed Gidan Dabino

Hadin Kai Ne Kadai Zai Kai Masana'antar Kannywood Tudun Mun Tsira -Ado Ahmed Gidan Dabino

LABARAI MASU NASABA

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

June 13, 2026
Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.