Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles), Ahmed Musa, ya magantu kan cece-kucen da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta dangane da yadda ya yi mu’amala da Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a ziyarar da ya kai gidan gwamnati a watan da ya gabata.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Musa ya durkusa wa gwamnan ba tare da yin musabaha ba, lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta.
- An Gano Dajin Da Ya Fi Shekara Miliyan Hudu A Duniya
- Kano Pillars Ta Kasa Zuwa Taka Leda Saboda Rashin Kuɗi
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a shafinsa na X (Twitter), Musa ya fayyace cewa, matakin nasa ya samo asali ne daga al’adun mutuntawa na gari, maimakon yadda wasu ke ganin cewa, rashin mutuntawa ga Gwamna Yusuf.
Ya jaddada cewa, a al’adun Arewacin Nijeriya, ayyuka irin su durkusawa suna nuna girmamawa ga masu daraja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp