• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Da Ya Sa Duniya Ke Bukatar Karfin Sin Na Samar Da Hajoji Masu Alaka Da Makamashi Mai Tsafta

by CGTN Hausa
2 years ago
sin

Kwanan baya, a gun taron makamashi na duniya karo na 26, babban darektan kamfanin Saudi Aramco, daya daga kamfanonin man fetur mafiya girma a duniya Amin H. Nasser, ya bayyana cewa, ana samun ci gaban alluna samar da wutar lantarki ta hasken rana bisa kokarin da Sin take yi na rage farashin su, kuma haka abun yake a fannin motoci masu amfani da makamashi mai tsabta.

A cewar mista Nasser, bunkasuwar sana’o’i masu alaka da makamashi mai tsafta a kasar Sin, ta hanzarta cimma burin kasashen yamma na samun daidaito tsakanin yawan hayaki mai dumama yanayi da za a fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin, kuma Sin ta taka rawar gani wajen karkata ga nau’o’in irin wadannan makamashi da za a iya amfani da su a nan gaba.

A halin yanzu, kasashe daban-daban na yin iyakacin kokarin zamanantar da masana’antun samar da hajoji, da amfani da makamashi mai tsafta, kuma ana matukar bukatar na’urori da sassan injuna dake da alaka da samarwa da amfani da makamashi mai tsabta.

Ban da wannan kuma, kafar yada labarai ta “Bloomberg” ta ba da labari a kwanan baya cewa, “nesa ta zo kusa” a fannin karkata hanyar da duniya ke bi ta amfani da makamashi, saboda yadda Sin take samar da hajoji masu alaka da makamashi mai tsabta masu saukin farashi.

Ya zuwa yanzu, yawan na’urorin samar da wutar lantarki ta amfani da karfin iska, da hasken rana da Sin take samarwa duniya, ya kai kashi 50% da 80%. Daga shekarar 2012 zuwa ta 2021, yawan karuwar ciniki ba tare da gurbata muhalli ba da Sin take gudanarwa ya kai kaso 146.3%, wanda ya karfafa bunkasuwar duniya, da kwarin gwiwa a bangaren samar da makamashi mai tsabta.

LABARAI MASU NASABA

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Kaza lika, Sin ta taimakawa sauran kasashen wajen daga karfin tinkarar sauyin yanayi ta hanyoyin samar da tallafin fasahohi, da inganta kwarewarsu da tallafin kudade da sauransu.

Wasu ‘yan siyasar Amurka suna fakewa da sunan wai “kasar Sin na samar da hajoji masu alaka da makamashi masu tsabta fiye da kima” wajen aiwatar da manufar kariyar ciniki, matakin da zai illata kokarin da ake yi na karkata hanyar amfani da makamashi a duniya.

Ko shakka babu, matsalar da duniya ke fuskanta ba samar da hajoji masu alaka da makamashi mai tsabta fiye da kima ba ne, domin kuwa ana matukar bukatar irin wadannan hajoji. Kuma Sin tana samar da su ga duniya bisa matsananciyar bukatar da ake da ita. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou
Daga Birnin Sin

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Next Post
Ko Tinubu Zai Hakura Da Ganduje Ya Rungumi Kwankwaso?

Ko Tinubu Zai Hakura Da Ganduje Ya Rungumi Kwankwaso?

LABARAI MASU NASABA

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.