Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin rufe daukacin asusun ma’aikatun jihar a ranar Laraba.
Abba, ya ba da umarnin ne yayin wani taro da ya hada da shugaban hukumar harajin jihar da shugabannin ma’aikatun gwamnati.
- Minista Ya Nemi A Ƙara Ƙulla Danƙon Zumunci A Tsakanin Nijeriya Da Kamfanin BBC
- An Gudanar Da Taron Wayewar Kai Ta Yanar Gizo Na Kasar Sin Na 2024 A Chengdu Na Sin
Ya bai wa Akanta-Janar na jihar, umarnin da ya rufe daukacin asusun adana kudaden ma’aikatun a wani mataki na tabbatar da kashe su ta hanyar da ta dace.
Ana kuma sa ran bankuna za su mika takardun shaidar bin wannan umarni daga fadar gwamnatin don a tabbatar an rufe asusun.
Gwamnan ya yi kira ga masu biyan haraji da su kwantar da hankalinsu yana mai ba su tabbacin cewa za a yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp