Shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC), Joe Ajaero ya ce da yiyuwar bukatar karin albashi mafi karanci ya lunka har zuwa miliyan daya a kowace wata lura da matsalolin rayuwa da tsadar kayan bukatu da ake fuskanta.
A cewar NLC, muddin matsatsin tattalin arziki ya ci gaba da tafiya a haka, babu shakka bukatunta zai sa ta nemi a biya mafi karancin albashi zuwa miliyan 1 a kowace wata ga ma’aikata.
- Sin Za Ta Kaddamar Da Gangamin Yayata Ci Gaban Mata
- Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Wasan Nijeriya Da Kyautar Filaye Da Gidaje Da Lambar MON Ta Kasa
A hirarsa da gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce, hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma karyewar darajar naira suna daga cikin dalilan da za su sanya kungiyar neman a biya albashi mafi karanci na miliyan 1.
Ya ce, “Wannan naira miliyan 1 din zai iya zama abun bukata muddin darajar naira ya ci gaba da karyewa. Matukar hauhawar rashin kayan bukatu suka ci gaba da tashi. Kungiyar Kwadago na tsayuwa ne bisa abubuwan da suke faruwa a cikin al’umma.
“Za ku tuna lokacin da muke tunanin naira 200,000, farashin canji ya kai zuwa naira 900. Amma yanzu da nake magana, farashin canji ya kai zuwa naira 1,400 koma fiye.
“Wadannan batutuwan su ne suke kai ga neman bukatar da muke da su, sannan ya shafi harkokin rayuwa, inda rayuwa ta yi matsatsi. Mun sha fada cewa bukatunmu za su tafi ne daidai da farashin tsadar rayuwa.
“Za ku amince da ni cewa farashin buhun shinkafa ya haura naira 60,000 zuwa naira 70,000. Kayan abinci na neman gagaran mutane. Yanzu, shin za mu samu mafi karancin albashin da ba zai ishemu na sufuri? “Muna da dukkanin wadannan batutuwan. Kuma hakan ne zai kai ga Sanya gwamnatin tarayya dukufa wajen wadannan yarjejeniyar,” ya shaida.
Wannan bayanan na Ajaero ya janyo barazanar tsunduma yajin aiki. Inda gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka shirya zaman tattaunawa domin baje batutuwan da suke akwai kan gargadin shiga yajin aikin kwanaki 14.
Kungiyoyin kwadagon sun zargi gwamnatin da yin kunnen uwar shegu da cimma yarjejeniyar da suka yi a baya.
Ya ce, “Sau daya tak a wata daya aka biya naira 35,000 ga ma’aikata.
Kuma, babu wani shaidar biyan wani ma’aikaci naira 25,000 a matsayin tallafi. Abun da ya haifar da abun da ke faruwa a ma’aikatar jin kai.
“Babu wani manomin da zai zo ya ce ya amshi taki daga wajen.