Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana haramta gaba ɗaya na shirye-shiryen siyasa da ake watsawa kai tsaye a duk wata kafar yada labarai. Kwamishinan yaɗa labarai, Comrade Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa matakin na da nufin hana yaɗa abubuwan da za su haifar da tarzoma da kuma kare al’adu da addini a jihar.
A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar, haramcin ba don takura wa ‘yan adawa ba ne, sai dai an yi ne don kare tsarkin al’adu da addinin mutanen Kano. An kuma sanya dokar cewa duk wani baƙo da ya fito a shirye-shirye dole ne ya sanya hannu kan alƙawarin guje wa kalaman batanci ko wuce gona da iri.
- Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta
- An Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Bayan Kwana 9 Da Aurensu A Kano
Ma’aikatar ta yi kakkausar gargadi ga masu gabatar da shirye-shirye kan yin tambayoyin da za su jawo hargitsi. Kwamishinan ya yaba da kafafen yaɗa labarai saboda raguwar abubuwan da suka saba wa ƙa’idoji tun bayan taron farko na kwata-kwata da aka yi.
Jihar na ci gaba da kamfen wayar da kai ga masu sharhi, da masu gabatar da shirye-shirye da Limamai, domin inganta yadda jama’a ke tattaunawa. Shugabannin kafafen yaɗa labarai sun yi alƙawarin ci gaba da haɗin gwuiwa da gwamnati.
Matakin ya zo ne bayan an lura da yawan shirye-shiryen siyasa masu jawo cece-ku-ce a jihar. Gwamnatin ta yi imanin cewa haramcin zai taimaka wajen rage tasirin rikice-rikicen siyasa a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp