Gwamnatin Jihar Zamfara ta yanke shawarar haramta zirga-zirga daga karfe 7:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe a kan iyakokin jihar da makwaftanta, Jihohin Katsina da Sakkwato.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Jihar, Manir Haidar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau ranar Talata.
Haidara ya ce an yanke wannan shawarar ne a yayin taron kwamitin tsaro na jihar.
- Hisba Ta Cafke Mata 7 Da Ake Zargi Da Satar Yadidduka A Kano
- Jihar Zamfara Ta Haramta Zirga-zirga A Tsakanin Iyakokinta Da Katsina Da Sokoto Daga Karfe 7 Na Yamma
Ya ce, “Ya zuwa yau (ranar Talata), gwamnatin jihar ta ba da umarnin hana zirga-zirga a kan iyakar Yankara da Jihar Zamfara da Jihar Katsina da kuma kan iyakar Bimasa Zamfara da Jihar Sokoto daga karfe 7:00 na safe. zuwa 6:00 na safe kullum.
“An yi hakan ne don magance matsalar sace-sacen matafiya a kan babbar hanyar Sakkwato zuwa Gusau-Funtua.”
“Wannan wani bangare ne na matakan da gwamnatin jihar ke dauka na ragewa tare da magance ayyukan sace-sacen da ‘yan bindiga ke yi, musamman a manyan titunan jihar,” in ji shi.
A cewar kwamishinan, an umurci dukkan masu ababen hawa da matafiya da su bi umarnin gwamnati.
“An umurci hukumomin tsaro da su sanya ido kan iyakokin biyu tare da tabbatar da cikakkiyar kulawa,” in ji shi.
…’Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud
A wani labarin kuma, a daren Litinin din da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada a lokacin da suke Sallar Tahajjud.
Sallar Tahajjud ibada ce da aka saba gudanarwa a cikin kwanaki 10 na karshen watan Ramadan gabanin ranar karamar sallah.
A cewar wani mazaunin unguwar mai suna Mannir wanda ya zanta da LEADERSHIP, maharan sun far wa masallacin ne a lokacin da ake Sallar dare.
Mannir, ya bayyana rashin tabbas game da ainihin adadin mutanen da aka kama.
Mannir ya kara da cewa “Yayin da har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda aka sace ba, hukumomi na ci gaba da bibiyar maharan.”
Har ya zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan kazamin hari, lamarin da ya kara janyo rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar karuwar ta’addanci da ayyukan ta’addanci a Jihar Zamfara. Idan dai za a iya tunawa, a mako guda da ya gabata ne Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da Shugaban Kasa Bola Tinubu domin shawo kan matsalolin tsaro da ke kara kamari a jihar.