HAJIYA BADIYYA MAGAJI INUWA, ita ce shugaba kuma wadda ta kafa gidauniyyar tallafa wa marasa karfi masu fama da larurur amosanin jinni ta hanyar ba su magunguna kyauta da ba su shawara, wato a turance ‘Sickle Cell Patients Health Promotion Centre’ (SCPHPC) da ke a Jihar Kaduna. Wakilinmu ABUBAKAR ABBA, ya tattauna da ita a kan nasarar yaki da cutar a karkashinta. Ga yadda ta kaya a tattaunawar:
Menene ya ja hankalin ki kika kafa da gidauniyar?
Yau shekararmu 15 da kafa gidauniyar wacce muke taimaka wa masu fama da larurar Amosanin Jini da magunguna ko wanne wata da kuma ba su shawarwari kyauta. Na kafa Giduniyar ce, bayan rasuwar dana da ya kamu da wannan larurar.
Na rasa ‘ya’yana biyu, dalilin da ya sa kenan, na kafa gidauniyar. Ni uwar ‘ya’ya ce masu wannan larurar, kuma wannnan gidauniyar ba wai Musulmi marasa karafin kadai muke tallafa wa ba, har da ma sauran mabiya Addinin Kirista da ‘ya’yansu suka kamu da larurar, bama nuna wani banbanci, domin duk wanda ka taimaka wa, kana da lada a gurin Allah kuma muna yin hakan ne, don mu kara wanzar da zaman lafiya a tsakanin sauran abokan zamanmu Kiristoci.
Wadanne irin nasarori kuka samu kika kafa ta?
Nasarori akwai masu dadi da marasa dadi. Mai dadin dai shi ne, tun daga lokacin da muka kafa gidauniyar a baya a gidan haya cibiyar take, sai dana na biyu wanda shi bai da larurar da abokansa da wasu ‘yanuwanmu suka hada kudi aka saya mana wannan gidan da muke tafiyar da ayyukan gidauniyar. Na biyu, tun daga lokacin da muka kafa gidauniyar har zuwa yau, ma’aikatana da masu yi min aikin sa kai, yau shekara 15, ba su gaji ba, ba albashi suke samu ba domin kullum ina gaya masu ladanmu na gurin Allah, kuma tun da na fara, abin bai taba tsayawa ba, komai yawan masu larurar muna tallafa masu da magunguna, kuma babu wanda ya taba tallafa mana ko da na Naira biyar.
Wadanne irin magunguna kuke ba masu irin wannan lalurar?
Maganin da muke ba su ba wai don ya warkar da su ba ne, sai dai don su zauna a cikin koshin lafiya. Farin cikina shi ne, da Allah ya tsaya mana muna ci gaba da taimaka wa masu larurar. Baya ga tallafawar da muke yi musu, muna kuma koya masu sana’oin hannu don su zama masu dogaro da kai, wani lokacin ma wadanda ke da bukatar karin jini, mu muke sayen jinin don a yi masu karin. Na yi tunanin yin hakan ne saboda kyamar auren da wasu mazan ke yi, musamman matan da ke dauke da larurar.
Ana yawan kiraye-kirayen gwajin jinni kafin aure, ko akwai wata rawa da kuke takawa ta wannan fuskar?
Tabbas, yadda masu shirin yin aure suka karbi shawarata na zuwa yin gwaji jininsu kafin yin aure don gudun kada su haifi masu larurar na daga nasarorin da muka samu bisa taimakawar kafofin yada labarai da malaman addinai a kan yadda muka sanar da su don su fadakar da ilmantar da masu shirin yin aure, kan mahimmancin zuwa yin gwajin jini kafin su yi aure. Masu son yin auren sun amsa wannan kiran na yin gwajin jini kafin a yi aure. A duk shekara idan muna yin taron zagayowar ranar masu fama da larurar da ake gudanar wa a duk ranar 19 ga watan Yuni, idan wakilan gwamnati sun zo gurin taron, muna ba su sako su kai wa gwamnati cewa, don Allah a kirkiro da doka da za ta sa sai an yi gwajin jini kafin a yi aure, domin ita ce hanya daya tilo, da za a kauce wa kamuwa da wannan larurar. Larura ce ba a daukar ta kowacce hanya sai daga jikin namji da macen da zai aura.
Ko kun taba kai maganar gaban majalisar dokoki ganin cewa su ne masu hakkin yin doka?
To Alhmdu lillahi, kamar shekara biyar da suka wuce, a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna el-Rufa’I, na aike da takarda zuwa ga Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna bisa nuna bukatar ‘yan majalisar su kikiro da doka da za ta tilasta sai masu son aure sun yi gwajin jini kafin su yi aure. An yi sa’a an yi dokar kuma el-rufa’i, ya sa hannu, amma a lokacin bai ce ga ranar da za ta fara aiki ba, saboda ka san sha’ani na siyasa wasu ‘yan siyasar za su iya nuna ra’ayinsu wasu kuma su nuna ba sa ra’ayi. Amma duk da hakan, da aka sanar a kafofin yada labarai na jihar, cewa gwamna ya karbi abin ya sa hannu, amma za a sa ranar a nan gaba, to tun da mutane suka ji da Kiristan da Musulmi, sai hamdala ga Allah na ce ko mutuwa na yi a waccan ranar, ina alfahari na yi wani abu dai. Yanzu abin da muka lura da shi shi ne, sai idan bayan an sa amarya a lalle ne, ake zuwa a yi gwajin jinin sai kuma sun riga sun hadu da angon bayan sakamon ya fito ya nuna akwai jininsu bai yi daidai ba, sai a ce ba za a fasa daura auren ba, wannan halin babu kyau cuta ce yi. Na sha gaya wa mutane, har kai kaka sai ka je ka rinka yin jinyyar jikan naka a asibiti.
A wata shekara kuma da muka yi taron zagayowar ranar, na bayar da shawara cewa, don Allah idan za a sa yara a makarantar firamare a tafi da takardar su ta samakakon gwajin jininsu don a tababatar da wanne irin jinsin jini suke da dauke da shi, idan kuma sun kai matakin sakandare, nan ma sai a kara daukar jininsu a yi gwaji cewa ya yi daidai sai a ajiye takardar gwajin, idan yaron ya girma ya riga ya san matsayin jininsa ban sani ko wasu sun fara amfani da wannan shawarar ba. Amman na san mu a Kaduna, gaskiya mun yi zarra wajen wayar da kai a kan larurar.
Baya ga Kaduna, akwai wasu wurare da suka ci gajiyar abin da kuke yi?
Tun daga lokacin da muka kafa giduniyar, yaran da muka taimaka wa masu fama da larurar, sun kai sama da 4000, wasu sun rasu wasu sun bar garin, wasu kuma ba a Kaduna suke da zama ba, ‘yanuwansu da ke a nan jihar ne da suka san a ‘yan uwan na suna da ‘ya’ya masu larurar suke kiransu suna ce masu akwai wata gidauniya a Kaduna da ke tallafa wa masu fama da larurar, sai iyayen su zo jihar su same mu tallafa wa ‘ya’yan na su da magungnan kyauta da kuma shawarwari.
To ganin ba za mu iya ci ga ba da tallafa wa ‘ya’yan nasu ba, tun da ba mu da karfi, tare da kuma matsalar kwaso ‘ya’yan nasu tun daga wasu jihohi zuwa wurinmu, sai na rinka rubuta masu irin magungunn da muke tallafa wa masu larurra don su kai zuwa asibitocin da suka fi kusa da su, don a taimaka masu da irin wadanan magungunan.
Muna kuma rokon gwamnati da ta sa mana hannu ba wai sai lallai da kudi ba, ko da magunguna ne, muna bukata, tun da bamu da wata ma’aikata da za mu ce muna samun riba don ci gaba da tafiyar da ayyukanmu, roko ne kawai muke yi don gudanar da ayyukan mu, yau da gobe wuya gare ta. Masu hannun da shuni suma muna neman taimkonsu, don maganar larurar nan, mutane za su zuba jarinsu don samun sakamako a gurin Allah.
Ko kun taba tunanin kafa rassa a kananan hukomi don amfanin mutanen da ke zaune a karkara?
Tun farko, hakan na daga cikin tsarinmu, wallahi da a ce gwamnati ta taimaka mana da mun yi hakan, domin larura ce da ta addabi ko ina musamman ma a Arewacin Nijeriya, ko da ma bamu bude rassa ba, da mun rika zuwa kananan hukumomi muna yin fadakarwa da wayar da kai akan larurar, amma har yanzu dai, ban fid da rai ba.