ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Rasa ‘Ya’yana Biyu Sanadin Amosanin Jini, Na Kafa Gidauniya —Hajiya Badiyya

by Abubakar Abba
3 years ago
Badiyya

HAJIYA BADIYYA MAGAJI INUWA, ita ce shugaba kuma wadda ta kafa gidauniyyar tallafa wa marasa karfi masu fama da larurur amosanin jinni ta hanyar ba su magunguna kyauta da ba su shawara, wato a turance ‘Sickle Cell Patients Health Promotion Centre’ (SCPHPC) da ke a Jihar Kaduna. Wakilinmu ABUBAKAR ABBA, ya tattauna da ita a kan nasarar yaki da cutar a karkashinta. Ga yadda ta kaya a tattaunawar:

Menene ya ja hankalin ki kika kafa da gidauniyar?
Yau shekararmu 15 da kafa gidauniyar wacce muke taimaka wa masu fama da larurar Amosanin Jini da magunguna ko wanne wata da kuma ba su shawarwari kyauta. Na kafa Giduniyar ce, bayan rasuwar dana da ya kamu da wannan larurar.
Na rasa ‘ya’yana biyu, dalilin da ya sa kenan, na kafa gidauniyar. Ni uwar ‘ya’ya ce masu wannan larurar, kuma wannnan gidauniyar ba wai Musulmi marasa karafin kadai muke tallafa wa ba, har da ma sauran mabiya Addinin Kirista da ‘ya’yansu suka kamu da larurar, bama nuna wani banbanci, domin duk wanda ka taimaka wa, kana da lada a gurin Allah kuma muna yin hakan ne, don mu kara wanzar da zaman lafiya a tsakanin sauran abokan zamanmu Kiristoci.

Wadanne irin nasarori kuka samu kika kafa ta?
Nasarori akwai masu dadi da marasa dadi. Mai dadin dai shi ne, tun daga lokacin da muka kafa gidauniyar a baya a gidan haya cibiyar take, sai dana na biyu wanda shi bai da larurar da abokansa da wasu ‘yanuwanmu suka hada kudi aka saya mana wannan gidan da muke tafiyar da ayyukan gidauniyar. Na biyu, tun daga lokacin da muka kafa gidauniyar har zuwa yau, ma’aikatana da masu yi min aikin sa kai, yau shekara 15, ba su gaji ba, ba albashi suke samu ba domin kullum ina gaya masu ladanmu na gurin Allah, kuma tun da na fara, abin bai taba tsayawa ba, komai yawan masu larurar muna tallafa masu da magunguna, kuma babu wanda ya taba tallafa mana ko da na Naira biyar.

ADVERTISEMENT

Wadanne irin magunguna kuke ba masu irin wannan lalurar?
Maganin da muke ba su ba wai don ya warkar da su ba ne, sai dai don su zauna a cikin koshin lafiya. Farin cikina shi ne, da Allah ya tsaya mana muna ci gaba da taimaka wa masu larurar. Baya ga tallafawar da muke yi musu, muna kuma koya masu sana’oin hannu don su zama masu dogaro da kai, wani lokacin ma wadanda ke da bukatar karin jini, mu muke sayen jinin don a yi masu karin. Na yi tunanin yin hakan ne saboda kyamar auren da wasu mazan ke yi, musamman matan da ke dauke da larurar.

Ana yawan kiraye-kirayen gwajin jinni kafin aure, ko akwai wata rawa da kuke takawa ta wannan fuskar?
Tabbas, yadda masu shirin yin aure suka karbi shawarata na zuwa yin gwaji jininsu kafin yin aure don gudun kada su haifi masu larurar na daga nasarorin da muka samu bisa taimakawar kafofin yada labarai da malaman addinai a kan yadda muka sanar da su don su fadakar da ilmantar da masu shirin yin aure, kan mahimmancin zuwa yin gwajin jini kafin su yi aure. Masu son yin auren sun amsa wannan kiran na yin gwajin jini kafin a yi aure. A duk shekara idan muna yin taron zagayowar ranar masu fama da larurar da ake gudanar wa a duk ranar 19 ga watan Yuni, idan wakilan gwamnati sun zo gurin taron, muna ba su sako su kai wa gwamnati cewa, don Allah a kirkiro da doka da za ta sa sai an yi gwajin jini kafin a yi aure, domin ita ce hanya daya tilo, da za a kauce wa kamuwa da wannan larurar. Larura ce ba a daukar ta kowacce hanya sai daga jikin namji da macen da zai aura.

LABARAI MASU NASABA

Abubuwa Shida Da Ya Kamata Mace Ta Sani Kafin Ta Yi Aure

Sirrin Mallakar Miji 

Ko kun taba kai maganar gaban majalisar dokoki ganin cewa su ne masu hakkin yin doka?
To Alhmdu lillahi, kamar shekara biyar da suka wuce, a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna el-Rufa’I, na aike da takarda zuwa ga Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna bisa nuna bukatar ‘yan majalisar su kikiro da doka da za ta tilasta sai masu son aure sun yi gwajin jini kafin su yi aure. An yi sa’a an yi dokar kuma el-rufa’i, ya sa hannu, amma a lokacin bai ce ga ranar da za ta fara aiki ba, saboda ka san sha’ani na siyasa wasu ‘yan siyasar za su iya nuna ra’ayinsu wasu kuma su nuna ba sa ra’ayi. Amma duk da hakan, da aka sanar a kafofin yada labarai na jihar, cewa gwamna ya karbi abin ya sa hannu, amma za a sa ranar a nan gaba, to tun da mutane suka ji da Kiristan da Musulmi, sai hamdala ga Allah na ce ko mutuwa na yi a waccan ranar, ina alfahari na yi wani abu dai. Yanzu abin da muka lura da shi shi ne, sai idan bayan an sa amarya a lalle ne, ake zuwa a yi gwajin jinin sai kuma sun riga sun hadu da angon bayan sakamon ya fito ya nuna akwai jininsu bai yi daidai ba, sai a ce ba za a fasa daura auren ba, wannan halin babu kyau cuta ce yi. Na sha gaya wa mutane, har kai kaka sai ka je ka rinka yin jinyyar jikan naka a asibiti.

A wata shekara kuma da muka yi taron zagayowar ranar, na bayar da shawara cewa, don Allah idan za a sa yara a makarantar firamare a tafi da takardar su ta samakakon gwajin jininsu don a tababatar da wanne irin jinsin jini suke da dauke da shi, idan kuma sun kai matakin sakandare, nan ma sai a kara daukar jininsu a yi gwaji cewa ya yi daidai sai a ajiye takardar gwajin, idan yaron ya girma ya riga ya san matsayin jininsa ban sani ko wasu sun fara amfani da wannan shawarar ba. Amman na san mu a Kaduna, gaskiya mun yi zarra wajen wayar da kai a kan larurar.

Baya ga Kaduna, akwai wasu wurare da suka ci gajiyar abin da kuke yi?
Tun daga lokacin da muka kafa giduniyar, yaran da muka taimaka wa masu fama da larurar, sun kai sama da 4000, wasu sun rasu wasu sun bar garin, wasu kuma ba a Kaduna suke da zama ba, ‘yanuwansu da ke a nan jihar ne da suka san a ‘yan uwan na suna da ‘ya’ya masu larurar suke kiransu suna ce masu akwai wata gidauniya a Kaduna da ke tallafa wa masu  fama da larurar, sai iyayen su zo jihar su same mu tallafa wa ‘ya’yan na su da magungnan kyauta da kuma shawarwari.

To ganin ba za mu iya ci ga ba da tallafa wa ‘ya’yan nasu ba, tun da ba mu da karfi, tare da kuma matsalar kwaso ‘ya’yan nasu tun daga wasu jihohi zuwa wurinmu, sai na rinka rubuta masu irin magungunn da muke tallafa wa masu larurra don su kai zuwa asibitocin da suka fi kusa da su, don a taimaka masu da irin wadanan magungunan.

Muna kuma rokon gwamnati da ta sa mana hannu ba wai sai lallai da kudi ba, ko da magunguna ne, muna bukata, tun da bamu da wata ma’aikata da za mu ce muna samun riba don ci gaba da tafiyar da ayyukanmu, roko ne kawai muke yi don gudanar da ayyukan mu, yau da gobe wuya gare ta. Masu hannun da shuni suma muna neman taimkonsu, don maganar larurar nan, mutane za su zuba jarinsu don samun sakamako a gurin Allah.

Ko kun taba tunanin kafa rassa a kananan hukomi don amfanin mutanen da ke zaune a karkara?
Tun farko, hakan na daga cikin tsarinmu, wallahi da a ce gwamnati ta taimaka mana da mun yi hakan, domin larura ce da ta addabi ko ina musamman ma a Arewacin Nijeriya, ko da ma bamu bude rassa ba, da mun rika zuwa kananan hukumomi muna yin fadakarwa da wayar da kai akan larurar, amma har yanzu dai, ban fid da rai ba.

Badiyya
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Badiyya
Adon Gari

Abubuwa Shida Da Ya Kamata Mace Ta Sani Kafin Ta Yi Aure

July 19, 2026
Sirrin Mallakar Miji 
Adon Gari

Sirrin Mallakar Miji 

January 25, 2026
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
Next Post
Mutum 547,774 Suka Cike Aikin Dansanda, Mako 1 Ya Rage A Rufe Shafin Daukar Aikin

Mutum 547,774 Suka Cike Aikin Dansanda, Mako 1 Ya Rage A Rufe Shafin Daukar Aikin

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.