• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja

by Abubakar Abba and Sulaiman
5 months ago
Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana kalubalen rashin tsaro a matsayin guda daga cikin dalilan da suka sa har yanzu ba a fara gudanar da aikin kamfanin takin zamani da ke yankin Zungeru na Karamar Hukumar Wushishi da ke jihar ba.

Babban Sakatare na ma’aikatar kasuwanci da zuba hannun jari da ke jihar, Alhaji Hamza Sarki Bello ne ya sanar da haka, a taron farko na majalisar zartawar jihar.

  • Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe
  • 2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

Alhaji Hamza, ya yi wannan furuci a wani taron manema labarai a fadar gwamantin jihar da ke Minna, babban birnin jihar a ranar Talatar da ta gabata.

Ya kara da cewa, duk da cewa; an zuba hannun jari na kimanin dala biliyan 12 a kamfanin, amma kalubalen rashin tsaro ya dakatar da fara gudanar da aikin.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar, ta sake sabunta yarjejeniyar da ta rabbta hannun na aikin, wacce gwamnatin da ta gabata ta jihar ta yi.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

“Gwamnatin ta yi hakan ne, sakamakon tabbatar da ganin an fara aiki a kamfanin daga nan zuwa karshen watan Mayun shekarar 2025.

“Gwamnatin Jihar da shude ce ta bai wa kamfanin kwangilar da kuma wani kamfani da ke Kasar Indiya aikin, inda gwamnatin ta zuba dala biliyan 12 a kamfanin,” in ji Hamza.

Sai dai, ya bayyana cewa; saboda kasancewar wasu dalilai, ba a samu cimma wata gagarumar nasarar a zo a gani ba a kan aikin.

Ya sanar da cewa, a watan da ya gabata ne, gwamnatin jihar ta sake yin nazari kan yarjeniyar ta baya da aka kulla, wadda kuma za a dawo, domin a ci gaba da yin aikin.

Babban Sakaren ya kara da cewa, manyan batutuwan da suka zama hummulhaba’isin dakatar da aikin su ne, kaluabalen rashin tsaro, amma yanzu, an sake yin nazari a kan sake dawo da ci gaba da aikin.

“An samar da daukacin Injinonin kamfanin, domin gudanar da aikin, amma kalubalen rashin tsaro ya jawo koma baya,” a cewar Babban Sakataren.

Ya yi nuni da cewa, idan aka fara gudanar da aikin, zai kara sanya wa manoman jihar samun wadataccen takin zamani, a kuma kan farashi mai rashusa.

Ita ma da take yi wa ‘yan jaridar karin bayani tun da farko, kwamishinan samar da bayanai da tsare-tsare, Binta Mamman ta bayyana cewa; an kara samar da tsaro a yankin, wanda hakan zai bai wa manoman jihar, damar komawa gonakinsu, domin fara aikin noma na bana.

“A shekarun baya, manoman jihar da dama, ba sa iya zuwa gonakinsu, domin yin noma, amma yanzu ba su da wata matsala ko fargaba wajen zuwa gonakin nasu, domin yin noma,” a cewar Binta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025
Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

Alkaluman GDP Na Sin Sun Fadada Zuwa Kaso 5.2 A Watanni 9 Na Farkon Bana

October 20, 2025
Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta

October 20, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.