Gwamnatin tarayya ta yi wa sababbin kungiyoyin jami’o’in Nijeriya guda biyu rajista a hukumance a matsayin kungiyoyin kasuwanci.
Wadanda suke kusa da lamarin sun bayyana cewa sababbin kungiyoyin sun kasance kishiyoyi ga kungiyar malaman jami’a’o’i ta kasa (ASUU), wadda da dage tana jayayya da gwamnatin tarayya.
- Kogin Kumadugu Ya Yi Ambaliya Karon Farko Cikin Shekara 100 A Yobe
- Gwamnatin Habasha Da ‘Yan Tawayen Tigray Za Su Zauna A Teburin Sulhu
Sababbin kungiyoyin da aka yi wa rajista dai sun hada da ‘Congressof Nigerian Unibersity Academics (CONUA), da ‘Nigeria Associationof Medical and Dental Lecturers in Academics (NAMDA).’
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gabatar da takardar yi wa kungiyoyin guda biyu rajista a Abuja, Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa wannan mataki yana kan tsarin dokar kasa domin shawo kan matsalolin da jami’o’in suke fuskanta.
Ngige ya kara da cewa wadannan kungiyoyi guda biyu wani bangare nena ASUU da suka balle daga jami’o’in Nijeriya, kamar yadda dokar kasa da kasa na kafa kungiyoyin mai lamba 87 da 98 ta tanada, wanda ya bai wa kungiyoyin ‘yancin kare hakkinsu.
Ngige ya ce, “Ma’aikatar kwadugo da samar da ayyukan yi ta yi gaban kanta wajen fito da sababbin kungiyoyin kasuwanci domin habaka tsarin kasuwanci a cikin kasar nan tare da yanke shawarar amincewa da yi wa sabbin kungiyoyi guda biyu rajista a karkashin jami’o’in Nijeriya.
“Watanni 8 da suka gabata, jami’o’in gwamnatin tarayya suna rufe, sannan dalibai suna zaune a gida sakamakon yajin aiki da kungiyar ASUU suke yi, duk da kokarin sasantawa da gwamnatin tarayya ta yi, amma lamarin ya ci tura.
“Karkashin dokar kasuwanci na gwamnatin tarayya ta shekarar 2004,wannan yajin aiki ya kamata ya kawo karshe tun a zaman sulhu da wannan ma’aikata da yi kokarin yi a ranakun 22 ga watan Fabrairun 2022 da ranar 1 ga watan Maris ta 2022.
“Duk wani kokarin sulhu ya ci tura, sakamakon dagewa da kungiyar ASUU ta yi wanda har kotun da’ar ma’aikata ta zantar da hukunci a matsayinta da take sasanta rikici a tsakanin kungiyoyi, amma ASUU ta ki bin wannan umarni.
“Abun ban sha’awar dai shi ne, mafi yawancin malaman jami’o’in da ke karantarwa a makarantun gwamnati sun nuna sha’awarsu na komawa bakin aiki idan aka sulhunta,” Ngige.
A nasa martanin, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa sababbin kungiyoyin da aka yi wa rajista ba mambobinsu ba ne, ya dai zargi gwamnatin tarayya da yin farfaganda wajen kare laifinta a wurin ‘yan Nijeriya.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya tana yin dukkkan wadannan abubuwa ne saboda mambobin ASUU sun ki rakonta kan tsayar musu da albashinsu.
Hakazalika, shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne mai wuka da nama na yanke hukunci na karshe kan yajin aikin ASUU bayan ganawarsa da zauran majalisar wakilai a wannan mako.
Ya dai bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala zaman ganawar sulhu tsakanin shugaban kasa da ‘yan majalisar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban majalisar wakilan yana fatan za a samu sulhu bayan gabatar da rahoto, inda ya roki shugabankasa ya yi nazari a rahoton kafin su sake zama da shi.